Kano: Dan kwangila ya kai shugaban karamar hukuma kara wurin EFCC kan rike mishi N14.9m

Kano: Dan kwangila ya kai shugaban karamar hukuma kara wurin EFCC kan rike mishi N14.9m

  • Wani dan kwangila, Mustapha Umar-Tallo ya kai wa ofishin EFCC takardu dauke da korafin shugaban karamar hukumar Gwarzo, Bashir Abdullahi da ke Kano
  • Ya bayar ga korafin ne sakamakon yadda Abdullahi ya ki biyan shi kudaden kwangilar da ya kammala na karamar hukumar duk da gwamnatin jihar ta saki kudin
  • Takardun sun bayyana yadda dan kwangilar ya biyo shi N25,009,243, sannan ya bayyana sauran ayyuka 12 da gwamnatin jihar ta biya kudaden su amma Abdullahi ya lamushe kudin

Kano - Wani dan kwangila, Mustapha Umar-Tallo ya mika takardu 2 zuwa ofishin hukumar yaki da rashawa ta EFCC, ya na zargin shugaban karamar hukumar Gwarzo, Bashir Abdullahi da kin biyan shi kudaden kwangilar da yayi na karamar hukumar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Umar-Tallo, ya rubuta takardar ta lauyan sa, Abubakar Lagazab, inda ya ke zargin shugaban karamar hukumar da kin biyan su kudaden duk da gwamnatin jihar ta riga ta biya kudaden.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

Kano: Dan kwangila ya kai shugaban karamar hukuma kara wurin EFCC kan rike mishi N14.9m
Ciyaman ya rike wa dan kwangila N14.9m, ya kai shi kara gaban EFCC. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

A takardar ta ranar 17 ga watan Nuwamba 2020 wacce ya bayyana ta ga manema labaran jihar Kano a ranar Alhamis, Umar-Tallo ya zargi shugaban karamar hukumar da lamushe kudaden ayyuka 20 na kwadago da ayyuka 14 na karamar hukumar.

Wani bangare na wasikar farkon ta zo kamar haka:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ayyukan 20 wadanda kudaden su ya kai N21,907,875 amma kuma ya biya ma N14,907,875. Mun hada wasikar da bayanan ayyukan har da na kudaden don karin bayani.
“Sauran ayyukan guda 14 na N10,101,368 ma har yau bai biya mu ko sisi ba. Yanzu gaba daya mu na bin shi N25,009,243 kuma gwamnatin jihar Kano ta dade da sakin kudin ayyukan. Idan ya na da korafi kuma zai iya kawo duk wasu takardun shaidar sa.

Dangane da yasar dukiyar jama’a kuma, takardar ta biyu mai dauke da kwanan wata 23 ga watan Nuwamban 2020 wacce ya yi irin korafin dai ta zo kamar haka:

Kara karanta wannan

Buhari: Sai bayan na sauka 'yan Najeriya za su gane irin gatan da na yi musu

“Yallabai, na tattaro bayanai dangane da ayyuka 12 wacce shugaban karamar hukumar Gwarzo ya amshi kudade daga hannun gwamnatin jihar Kano ya na nuna kamar ya biya amma kuma ya lamushe”.
“A bisa korafin da na yi, ayyuka 7 da na lissafo na N423,561,188 wadanda har yanzu bai yi ayyukan ba,” kamar yadda takardar ta zo.

Majiya daga ofishin EFCC ta sanar da manema labarai cewa tuni hukumar ta gayyaci shugaban karamar hukumar zuwa ofishin su don ya amsa tambayoyi, Daily Nigerian ta wallafa.

Bagudu: Wasu kasashen su na da wurin kiwo da ya fi girman wasu jihohin Najeriya

A wani labari na daban, Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya ce wasu kasashe suna da wuraren kiwo da suka fi wasu jihohi a Najeriya girma.

Ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa kan rikicin makiyaya da Fulani a gidan talabijin na Channels da aka yi da shi.

Kara karanta wannan

Survival Fund: Gwamnati ta raba wa 'yan Najeriya sama da miliyan 1 kudade N56.8bn

A cikin kwanakin nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarni ga kwamiti da a sake duba yadda za a samar da wuraren kiwo 368 a jihohi 25 na kasar nan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel