Bagudu: Wasu kasashen su na da wurin kiwo da ya fi girman wasu jihohin Najeriya
- Atiku Bagudu, gwamnan jihar Kebbi ya ce akwai kasashen da ke da manyan wuraren kiwo killatattu
- Kamar yadda ya sanar a tattaunawar da aka yi da shi a ranar Alhamis, wuraren kiwon sun fi wasu jihohi a kasar nan girma
- Ya goyi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari kan umarnin da ya bada na kafa wuraren kiwo 368 a jihohi 25
Kebbi - Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya ce wasu kasashe suna da wuraren kiwo da suka fi wasu jihohi a Najeriya girma.
Ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa kan rikicin makiyaya da Fulani a gidan talabijin na Channels da aka yi da shi.
A yayin kare umarnin shugaban kasa Muhammadu kan samar da wuraren kiwo a kasar nan, Bagudu ya ce dubawa tare da gane hanyoyin kiwo zai taimaka wurin shawo kan matsalar makiyaya da manoma.
A cikin kwanakin nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarni ga kwamiti da a sake duba yadda za a samar da wuraren kiwo 368 a jihohi 25 na kasar nan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, wannan ya faru ne har da jajircewar wasu bangarori na kasar. Amma Bagudu ya ce umarnin shugaban kasan bai hana kiwon ba kwata-kwata.
"Kwamitin zai duba hanyoyin kiwo kuma ya yi aiki da jihohi wurin gina su. Hakan zai sa a gano yawan matsalar."
"Shugaban kasan ya na da ra'ayi wurin duba wuraren kiwo. Aiki ne na sa kai kuma dole ne a hada kai da jihohi. Jama'a na cewa mun yi magana kan kiwo. Tabbas, amma mene ne wurin kiwo? Ba a kiwo a iska, ana yin shi ne a fili.
"A wasu kasashen kamar su Australia, wuraren kiwo sun fi wasu jihohin Najeriya girma. Toh don haka ta yaya ake gane abinda akwai? Ya ya za a yi a zamanantar da su?
Bagudu: Muguntar 'yan bindiga ta fi shafar Fulani, ba mu sauraron labaransu ne kawai
A wani labari na daban, Atiku Bagudu, gwamnan jihar Kebbi, ya ce matsalar garkuwa da mutane tare da satar shanu a kasar nan ta fi shafar Fulani.
A yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, Bagudu ya ce jama'a ba su sauraron abinda Fulani ke fuskanta a bangare garkuwa da su ko kuma sace musu shanu.
A cikin shekarun da suka gabata, Fulani makiyaya ake zargi da kai farmaki tare da sace jama'a, lamarin da ya kawo rikicin kabilanci. Amma sai dai a koda yaushe Fulani suna cigaba da musanta cewa su ke da alhakin wannan hare-haren.
Asali: Legit.ng