Buhari: Sai bayan na sauka 'yan Najeriya za su gane irin gatan da na yi musu

Buhari: Sai bayan na sauka 'yan Najeriya za su gane irin gatan da na yi musu

  • Shugaba Buhari ya bayyana cewa, 'yan Najeriya za su yi kewar yadda ya tafka aiki bayan ya bar ofis
  • Shugaban ya bayyana haka ne yayin wani bikin a fadar gwamnati kan lamurran tattalin arzikin kasa
  • Shugaban ya kuma kaddamar da sabon sashe a hukumar zuba hannun jari ta Najeriya (NSIA)

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya ce za a ji tasirin aikin da ya tafka a Najeriya bayan ya bar ofis a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ya fadi haka ne bayan kaddamar da sabuwar gudanarwar Hukumar Zuba Jari ta Najeriya (NSIA).

A takaitaccen biki da aka gudanar a fadar gwamnati, Abuja, Buhari ya umarci hukumar da ta kara saka hannun jari da ke tallafawa fadada tattalin arziki, saboda an yi hasashen farashin mai na duniya zai ragu zuwa kusan dala 40 a kowace ganga nan da shekarar 2030.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hallaka dan Sanata Bala Na'Allah da aka yi

Shugaban ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na aiwatar da ayyuka na dogon lokaci da shirye-shiryen da ke samar da ayyukan yi ga 'yan Najeriya.

Buhari: Sai bayan na sauka 'yan Najeriya za su gane irin gatan da na yi musu
Shugaban kasar Naejriya, Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce cikakken tasirin yawancin ayyukan dabarun da aka fara karkashin kulawarsa za a ji tasirinsu ne kawai bayan ya bar ofis.

Ya bayyana nadin kwamitin mutum 9 a matsayin kira ga aiki, aiki da aiwatarwa, ya kara da cewa sun kware sosai kan aikin da aka basu.

A cewar shugaba Buhari:

“Wannan Gwamnatin tana aiki a kan manufar canji na dogon lokaci wanda duk mun yarda da hakan ba makawa. Canji na faruwa ko an shirya ko ba a shirya ba."

'Yan APC sun roki Buhari ya mika kujerarsa zuwa kudancin Najeriya a zaben 2023

A bangare guda, wata kungiya a jam'iyyar APC mai suna South East Mandate (SEM), ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saukaka hanyoyin zabar dan takarar shugaban kasa daga amintattun mambobin jam’iyyar na Kudu maso Gabas a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Raba-gari: A karshe Shugaba Buhari ya bayyana wadanda ke daukar nauyin IPOB

Ta ce manufarta ita ce tabbatar da an samu shugaba daga yankin na Kudu maso Gabas a matsayin wanda zai gaji Shugaba Buhari, Daily Sun ta ruwaito.

Kungiyar ta bukaci jam’iyyun siyasa a Najeriya da su mika tikitin takarar shugaban kasar nan zuwa Kudu maso Gabas bisa adalci, gaskiya da lamiri mai kyau.

Survival Fund: Gwamnati ta raba wa 'yan Najeriya sama da miliyan 1 kudade N56.8bn

A wani labarin, Maryam Katagum, karamar ministar masana’antu, kasuwanci da saka hannun jari, ta ce gwamnatin tarayya ta raba naira biliyan 56.8 ga mutane sama da miliyan 1 - ciki har da wadanda aka yi wa rajista a karkashin Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni (CAC).

Ministar, wacce kuma itace shugabar kwamitin kula da shirin Survival Fund, ta fadi hakan ne a wani taron manema labarai a ranar Talata 31 ga watan Agusta a Abuja, The Cable ta tuwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Ta kuma kaddamar da shirin da a cewarta, shine na karshe a shirin kananan sana'o'i da kananan masana'antu (MSMEs).

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.