Survival Fund: Gwamnati ta raba wa 'yan Najeriya sama da miliyan 1 kudade N56.8bn
- Gwamnatin Tarayya ta raba wa 'yan Najeriya sama da dubu 100 kudade a karkashin shirin Survival Fund
- Gwamnati ta kirkiri shirin ne domin tallafawa kasuwanni da ma'aikatun da Korona ta jikkata
- Maryam Katagum, karamar ministar masana’antu, kasuwanci da saka hannun jari ta bayyana nasarar da aka samu
Abuja - Maryam Katagum, karamar ministar masana’antu, kasuwanci da saka hannun jari, ta ce gwamnatin tarayya ta raba naira biliyan 56.8 ga mutane sama da miliyan 1 - ciki har da wadanda aka yi wa rajista a karkashin Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni (CAC).
Ministar, wacce kuma itace shugabar kwamitin kula da shirin Survival Fund, ta fadi hakan ne a wani taron manema labarai a ranar Talata 31 ga watan Agusta a Abuja, The Cable ta tuwaito.
Ta kuma kaddamar da shirin da a cewarta, shine na karshe a shirin kananan sana'o'i da kananan masana'antu (MSMEs).
Shirin wani bangare ne na shirin dorewar tattalin arzikin Najeriya (NESP) wanda kwamiti karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya samar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Katagum ta yi bayanin cewa shirin ya nufi masu cin gajiya 100,000, amma kamar yadda a lokacin da aka rufe kafar neman tallafin, bayanan mutane 65,976 ne kawai aka karba, wanda 50,032 daga ciki suka tsallake jarabawar share fage sannan aka tantance su.
A cewarta:
"Zuwa yau, mun yi nasarar raba adadin kudi N56,842,780,000.00 zuwa mutum 1,079,323 gami da wadanda aka yiwa rajista karkashin CAC."
"Gwamnatin tarayya na shirin fitar da sashin karshe na shirin wanda aka sani da tsarin tallafin gaggawa GOS)."
Ministar ta ce barkewar Korona ya haifar da raguwar bukatun kamfanoni da samfuran gida da kayayyaki, ta kara da cewa an tsara shirin ne don taimakawa kananan masana'antu.
Katagum ta yi bayanin cewa an jinkirta fara aikin ne saboda lamuran wasu shirye-shirye kamar rashin biyan kudi, daidaita wasu bangarori da tabbatar da daidaito tsakanin jihohi.
Dangane da batun tantancewa da duba cancanta, ministar ta ce dole ne wadanda za su ci gajiyar su kasance 'yan Najeriya da ke da BVN kuma suna da karfin ma'aikata da ba su gaza uku ba.
Ministar ta ce shirin ya kuma samu babban ci gaba a wasu tsare-tsare.
Gwamnatin Buhari ta fara kaddamar da shirin N-Power a karo na uku
Gwamnatin tarayya a ranar Litinin 23 ga watan Agustan 2021 ta fara kaddamar da shirin N-Power rukunin C shashi na farko, The Nation ta ruwaito.
Ma'aikatar agaji da ayyukan jin kai ta kasa ta fara aikin yin rajista na rukuni na uku na masu cin gajiyar shirin a ranar 26 ga Yuni, 2020.
Ministar agaji da ayyukan jin kai, Sadiya Farouq ta ce sama da mutum miliyan shida suka nuna sha'awarsu ga cin gajiyar shirin.
Ta ce rukunin C zai dauki mutane 510,000 don cin gajiyar shirin sashi na farko da kuma mutane 490,000 a sashi na biyu.
Sabon bayani: Duk wanda aka zaba a shirin N-Power ya je ya yi 'Biometric'
A wani labarin, Gwamnatin tarayya, ta hannun ma’aikatar ayyukan jinkai da ci gaban zamantakewa, ta fitar da sabbin bayanai kan shirin N-Power Batch C (stream 1).
Legit.ng ta rahoto cewa bayanan da ke kan shafin yanar gizo na ma'aikatar, https://nasims.gov.ng/, na nuna cewa ana bukatar duk wadanda aka zaba a shirin da su gaggauta shigar da bayanan zanen yatsun hannus (Biometric) don samun cancantar shiga matakin karshe na shirin.
Ma'aikatar ta bayyana wasu hanyoyi da ya kamata wadanda aka zaban za su bi wajen ba da bayanan nasu, wanda zai bukaci shigar da zanen yatsun hannu da aka sani da Biometric a turance.
Asali: Legit.ng