ISWAP ta yi ikirarin harba rokar Katyusha a Mallam Fatori sau 4 a mako 1

ISWAP ta yi ikirarin harba rokar Katyusha a Mallam Fatori sau 4 a mako 1

  • Mayakan ISWAP wadanda aka fi sani da Boko Haram sun yi ikirarin jefa roka a garin Mallam Fatori a jihar Borno
  • ‘Yan ta’addan sun kai wa sansanonin soji farmaki sakamakon harin har suna hallaka sojoji 5 a garin
  • An samu wannan bayanin ne a wata takarda ta ranar 1 ga watan Satumba wacce ISWAP ta fitar

Mallam Fatori, Borno - Mayakan ISWAP wadanda aka fi sani da Boko Haram sun harba roko zuwa Mallam Fatori da ke jihar Borno har sau hudu a cikin mako daya tak.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda ‘yan ta’addan sun kai wa sansanonin farmaki a harin wanda ya yi sanadiyyar salwantar sojoji 5.

ISWAP ta yi ikirarin harba rokar Katyusha a Mallam Fatori sau 4 a mako 1
Mayakan ta'addanci na ISWAP a kan motar yaki. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

A wata takarda wacce IS ta saki a ranar 1 ga watan Satumba, ‘yan ta’addan ISWAP sun ce sun dade suna harba roka sansanin soji da ke Mallam Fatori kuma sun hallaka sojoji 4 kenan tun ranar 25 daga watan Augusta.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Najeriya sun ragargaji yan ta'addan ISWAP a Borno, sun kashe 6

“Ubangiji Allah ya bai wa sojoji masu jihadi nasara akan sansanin soji cikin kwana biyu da suka gabata a garin Mallam Fatori da ke jihar Borno, sakamakon harba rokar Katyusha.
"Kuma ta isa inda muka aikata, mun gode wa Allah,” kamar yadda takardar da suka saki a ranar 2 ga watan 2 na Satumba wacce Daily Nigerian ta gani ta ce.

A ranar 2 ga watan Satumba, kungiyar ta saki hotuna 6 wadanda suke nuna mayakan suna harba roma a sansanin sojin garin da suka bayyana.

'Yan sanda sun bindige Buba Baromi, kasurgumin mai kai wa 'yan bindiga bayanai a Niger

A wani labari na daban, jami'an rundunar yaki da 'yan bindiga ta 'yan sandan jihar Niger sun bindige gagararren mai kai wa 'yan bindiga bayanai, Buba Baromi. An sheke Baromi ne a wata maboyarsa da ke dajin Damba na jihar Niger, PRNigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

ISWAP ta yi ikirarin sheke sojin Najeriya 10, sace makamai da alburusai a Rann

PRNigeria ta tattaro cewa, wasu mafarautan yankin sun jagoranci 'yan sanda maboyar Baromi inda ya ke jinyar wani harbin bindiga da aka yi masa yayin wata arangama da yayi da jami'an tsaro a baya.

Wani jami'in sirri da aka yi aikin da shi, ya sanar da PRNigeria cewa, Baromi ba bayanai kadai yake kai wa 'yan bindiga ba, har jagorantarsu yake yi zuwa wurin da za su kai farmaki kuma su sace jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel