Dakarun Sojin Najeriya sun ragargaji yan ta'addan ISWAP a Borno, sun kashe 6
2 - tsawon mintuna
- Sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka yan ta'ddan Boko Haram shida
- Yan ta'addan na dauke da kayan abinci da barasa da zasu kaiwa yan'uwansu
- Sojin sun kwace makamai da Albursai da kuma buhuhunan tabar wiwi
Borno - Dakarun hukumar Sojojin Najeriya dake yaki da ta'addan a yankin Arewa maso gabas sun samu nasarar hallaka yan ta'adda shida ranar Laraba, 1 ga watan Satummba, 2021.
Kakakin hedkwatar tsaron Najeriya Onyeama Nwachukwu ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis a shafin hukumar na Facebook.
Yace:
"Rundunar 25 Birgade karkashin Operation HADIN KAI (OPHK) ta kashe yan ta'addan ISWAP 4 a ranar Laraba, 1 ga Satumba, 2021."
"Yan ta'adan sun yi arangama da Sojoji masu sintiri ne a Kukawa inda akayi musayar wuta har aka kashesu. Sojojin sun kwato bindigogin AK47 guda 4, magazin 4 dauke da albursai kowani guda 30."
"A wani harin kuma da rundunar 195 Bataliya suka kai tare da hadin kan CJTF da garejin Dusman-Muna a jihar Borno, an kashe yan ta'addan ISWAP biyu."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Me suka kwato hannunsu?
Onyeama ya bayyana yadda dakarun Sojin suka kwace makamai, albursai da buhuhuna na barasa.
Hakazalika ya ce sun lalata manyan motocin yan ta'addan da ke amfani da su wajen kai kayayyakin abinci.
A cewarsa:
"Sojojin sun lalata motocin ISWAP dake dauke da kayan abinci da barasa. Abubuwan da aka samu sun hada da buhun wiwi 2, buhun sabulun wanki 2, kwalin maganin sauro 120, ragar kariya daga cizon sauro 12 da atamfa biyu.
"Sauran sune kekuna biyu, buhun wake biyu, buhun masara daya da kuma wasu kifaye."
Asali: Legit.ng