Shugaba Buhari ya sabunta naɗin magatakardan hukumar TRCN

Shugaba Buhari ya sabunta naɗin magatakardan hukumar TRCN

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sabunta nadin Farfesa Segun Ajiboye a matsayin magatakardan TRCN
  • Zai cigaba da rike wannan mukamin ne na tsawon wasu shekaru 5 kamar yadda ya amshi takarda a ranar Talata
  • Ya amshi takardar ne ta hannun sakataren ma’aikatar ilimi, Architect Sunday Echono

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sabunta nadin Farfesa Segun Ajiboye na tsawon shekaru 5 a matsayin magatakardan hukumar yi wa malamai rajista, TRCN.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Ajiboye ya amshi takardar a ranar Talata ta hannun sakataren ma’aikatar ilimi, Architect Sunday Echono.

Shugaba Buhari ya sabunta nadin magatakardan hukumar TRCN
Buhari ya sabunta nadin magatakardan hukumar TRCN. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

Kamar yadda VON suka ruwaito, Ajiboye ya yi godiya ga shugaban kasa a kan yadda ya yadda da aikinsa kuma ya yi imani da cewa ya na aiki tukuru har ya kara masa shekaru 5 ya cigaba daga inda ya tsaya.

Kara karanta wannan

Tsohon ministan Afghanistan ya koma sana'ar siyar da abinci a kasar Jamus

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Ajiboye ya kada baki ya ce tabbas bukatar maje hajji sallah, don haka zai ci gaba da dage wa wurin bunkasa aikin koyarwa har sai ya bunkasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa, zai kara shekaru 5 wurin ganin ya samar wa malaman Najeriya walwala sannan ya wayar da su a kan sababbin hanyoyin koyarwa na zamani.

Ajiboye ya yi godiya ga ma’aikatan TRCN inda yace sun ba shi hadin kai kwarai, idan bacin bashi kwarin guiwa da bai samu wannan nasarar ba.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, Adeboye ya ce:

Ina so in yi godiya ga shugaban kasa a kan yarda da ni da ya yi dari bisa dari har ya na sabunta nadi na. Shugaban kasa ya kara ba ni wata jarabawar don ya ga dagiya ta, kuma matsawar ina tare da ma’aikatar TRCN, tabbas za mu yi ayyuka tukuru.

Kara karanta wannan

Rikicin Siyasa: Ina Nan Daram a Kan Kujerata, Shugaban PDP Ya Maida Martani

Nan da shekaru 5, malamai za su kara samun walwala da cigaba a zamanance. Za mu kara gyara harkar koyarwa don ingancin ilimin Najeriya ya hauhawa har ya zama cikin mafi inganci a duniya.

Na ƙosa in ga ka yi nasara, Buhari ya faɗa wa ɗan takarar gwamnan APC a Anambra, Andy Uba

A wani labari na daban, shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata, ya faɗa wa Sanata Andy Uba, ɗan takarar Jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Anambra cewa ya ƙosa ya ga an zabe shi gwamna, The Cable ta ruwaito.

An shirya gudanar da zaben ne dai a ranar 6 ga watan Nuwamban 2021 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaba Buhari, wanda ya yi magana a gidan gwamnati, Abuja yayin tarbar Sanata Uba, ya ce:

Ina farin cikin maraba da kai a jam'iyyar mu a hukumance. Ina maka fatan alheri. Na ƙosa in ga ka yi nasara, kuma za mu riƙa bibiyar lamarin."

Kara karanta wannan

Obasanjo: Masu son ganin rabewar kasar nan makiyanta ne, za su ji kunya

Asali: Legit.ng

Online view pixel