Na ƙosa in ga ka yi nasara, Buhari ya faɗa wa ɗan takarar gwamnan APC a Anambra, Andy Uba

Na ƙosa in ga ka yi nasara, Buhari ya faɗa wa ɗan takarar gwamnan APC a Anambra, Andy Uba

  • Shugaba Buhari ya gana da Sanata Andy Uba, ɗan takarar gwamnan APC a zaben jihar Anambra da ke tafe
  • Shugaban kasar ya yi maraba da Sanata Uba zuwa APC, ya kuma ce ya ƙosa ya ga ya yi nasara a zaben gwamnan
  • Shugaban kwamitin riko na APC, kuma Gwamnan Yobe Mai Mala Buni da wasu muƙarraban APC ne suka yi wa Uba rakiya

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata, ya faɗa wa Sanata Andy Uba, ɗan takarar Jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Anambra cewa ya ƙosa ya ga an zabe shi gwamna, The Cable ta ruwaito.

An shirya gudanar da zaben ne dai a ranar 6 ga watan Nuwamban 2021 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Na ƙosa in ga ka yi nasara, Buhari ya faɗa wa ɗan takarar gwamnan APC, Andy Uba
Gwamna Hope Uzodinma na Jihar Imo, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, Shugaba Muhammadu Buhari, Sanata Andy Uba da Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Shugaba Buhari, wanda ya yi magana a gidan gwamnati, Abuja yayin tarbar Sanata Uba, ya ce:

"Ina farin cikin maraba da kai a jam'iyyar mu a hukumance. Ina maka fatan alheri. Na ƙosa in ga ka yi nasara, kuma za mu riƙa bibiyar lamarin."

Su wanene suka yi wa Andy Uba rakiya ganin Buhari?

Shugaban kwamitin riƙon ƙwarya na APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni na daga cikin wadanda suka yi wa Andy Uba rakiya.

Sauran sun hada da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, Gboyega Oyetola ka jihar Osun, Hope Uzodinma na jihar Imo, Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas da wasu muƙarraban gwamnati.

Gwamna Buni ya ce APC na samun sabbin mambobi a kowanne rana daga jihar Anambra, yana mai nuni da sauya shekar Stella Oduah da Joy Emordi, ya ƙara da cewa lokaci ya yi da za su karɓi Anambra kuma za su yi aiki tare.

Gwamna Uzodinma ya bawa shugaban kasar tabbacin cewa zai kai wa mutanen Anambra saƙon jam'iyyar APC, "wadda za ta haifar mana da nasara a Nuwamba."

Ya kuma yi wa shugaban kasar godiya saboda saukaka masa aikinsa, "domin nagartarsa da dattaku a Nigeria. Sunan ka na bude mana kofofi duk inda muka tafi kuma mutane na shigowa jami'yyar mu a yau saboda hakan."
"Da izinin Allah, za mu yi nasara," a cewar Uzodinma cikin wata sanarwar da kakakin shugaban kasa Femi Adesina ya fitar

2023: Ba mu buƙatar Atiku ya sake takara, Ya tafi Dubai ya manta da mu tunda ya sha kaye a 2019, Ƙungiyar PDP

A wani labarin daban, wata kungiya mai suna People’s Democratic Party (PDP) Action 2023, ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kada ya sake takara a shekarar 2023 don ya yi watsi da jam'iyyar ya koma Dubai, UAE, tunda ya fadi zabe a 2019, rahoton Daily Trust.

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, bai riga ya bayyana niyarsa na son sake takara ba a 2023, amma, dansa, Adamu Atiku Abubakar, ya tabbatar cewa zai sake takara.

Amma a martaninsa, Atikun ya ce ba watsi da jam'iyyar ta PDP ya yi ba, ya tafi yin karatun digiri na biyu ne a kasar waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel