Rikicin Siyasa: Ina Nan Daram a Kan Kujerata, Shugaban PDP Ya Maida Martani
- Shugaban jam'iyyar PDP ta kasa, Prince Uche Secondus, yace yana nan daram a kan mukaminsa
- Shugaban ya bayyana cewa labarin da ake yaɗawa cewa bai je taron NEC ba saboda ya sauka ba gaskiya bane
- Yace ya ki zuwa taron ne domin biyayya ga umarnin kotu, amma mulkinsa zai kare ne a watan Disamba
Abuja - A kokarin da yake na rike matsayinsa, Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, ya musanta rahoton cewa ya yi murabus, kamar yadda punch ta ruwaito.
A wani jawabi da kakakinsa, Ike Abonyi, ya fitar ranar Asabar, yace ya kauracewa taro majalisar zartarwa na PDP ne domin biyayya ga umarnin kotun jihar Cross Rivers, wacce ta hana shi jagorantar ayyukan shugabanci.
Kotun ta bada umarnin dakatarwar ne ranar Jumu'a, kuma wannan shine karo na uku da kotu ta yanke hukunci a kan Secondus cikin mako ɗaya.
Yaushe Secondus zai gama mulkinsa?
A cikin jawabin, Secondus yace zangon mulkinsa na shekara 4 zai kare ne a watan Disamba 2021, bayan an zaɓe shi a Disamba 2017.
Yace:
"Ofiishin yaɗa labarai na Prince Uche Secondus, na son yin karin haske kan karyar da ake yaɗawa cewa ya sauka daga mukaminsa na shugaban PDP."
"Rashin ganin Secondus a wurin taron jam'iyya da aka gudanar ranar Asabar ya faru ne domin biyayyarsa ga umarnin babbar kotun jihar Cross Rivers."
"A matsayinsa na ɗan kasa na gari mai bin dokokin kasa, shi yasa ba'a hange shi a wurin taron ba domin biyayya ga umarnin. Zangon mulkin Secondus zai kare ne a ranar 10, ga watan Disamba."
Umarnin kotu daban-daban kan Secondus
Wata kotu a jihar Rivers, dake zamanta a Patakwal, ta bada umarnin dakatar da shugaban PDP daga baki ɗaya ayyukan shugabancin PDP, kamar yadda premium times ta ruwaito.
Sai dai kwana hudu kacal bayan faruwar haka, babbar kotun jihar Kebbi dake Birnin Kebbi, ta maida shi kan karagar mulkinsa.
Saboda hukuncin kotu na baya-baya a Cross River, Secondus ya umarci mataimakinsa na kudu, Yemi Akinwonmi, ya jagoranci taron NEC.
A wani labarin kuma FG Ta Fara Rabawa Talakawa Masu Karamin Karfi N20,000, Ta Bayyana Rukunin Mutanen da Zasu Amfana
Gwamnatin tarayya ta fara biyan hakkokin yan Najeriya da suka amfana da shirin tallafi na CCT.
Shugabar sashin shirin reshen jihar Kogi, Mrs Falilat Abdurasaq, tace an fara biyan N20,000 na tsawon wata huɗu.
Asali: Legit.ng