PDP: Gwamnatin Buhari na amfani da EFCC wajen cin zalin 'yan adawarta na PDP

PDP: Gwamnatin Buhari na amfani da EFCC wajen cin zalin 'yan adawarta na PDP

  • Jam'iyyar PDP ta zargi APC da gwamnatin Buhari wajen cin zarafin mambobin PDP a kasar
  • PDP ta ce, gwamnatin Buhari na amfani da EFCC wajen bata sunan mambobin jam'iyyar PDP
  • Hakazalika, ta ce, gwamnatin APC na razanawa da kuma kokarin tilasta mambobin PDP dawowa APC

Abuja - Jam’iyyar PDP ta zargi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da amfani da hukumomin tsaro don murkushewa da cin zalin ‘yan adawa, The Cable ta ruwaito.

A cikin wata sanarwa da Kola Ologbondiyan, kakakin PDP ya fitar a ranar Asabar 21 ga watan Agusta, ya ce jam’iyyar APC na amfani da hukumar EFCC don cin zarafin shugabannin PDP “a sabon yunkurin murkushewa da raunana samuwar adawa”.

Ologbondiyan ya ce jam’iyyar APC tana kai hare-hare kan masu maganan da ba sa tare da su don “tayar da yanayi na rashin bin tsarin dimokradiyya” a kasar kafin zaben shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Bayan ya koma APC, ‘Ya ‘yan Jam’iyya sun fara rigima da Yakubu Dogara a jihar Bauchi

PDP: Gwamnatin Buhari na amfani da EFCC wajen cin zalin 'yan adawarta
Kola Ologbondiyan | Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Hakazalika, ya bayyana cewa, duk irin wadannan abubuwa ba za su hana jam'iyyar PDP da 'ya'yanta ba wajen ayyukanta na karbe mulki a 2023 domin kai Najeriya ga tudun mun-tsira.

A wani yankin sanarwar na cewa:

“Jam’iyyar APC ta san cewa 'yan Najeriya sun yi gaji da ita saboda gazawa da ta yi kuma babu yadda za a yi ta ci zabe a kowane irin yanayi.
“Don haka, take neman yin amfani da tsarin mulki na kasar don ragewa da murkushe adawa da muryoyin da ba sa tare da su da kuma tayar da hankulan dimokuradiyya kan 'yan Najeriya.

EFCC ake amfani da ita wajen bata manyan PDP

Yayin da PDP ke bayyana kara cewa, ana amfani da EFCC wajen bata mambobinta da razana su, yankin sanarwar da Nigerian Tribune ta ruwaito ya ce:

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Rikicin cikin gidan da ya ke damalmala Jam’iyyar APC ya kara cabewa

“Wani bangare na wannan mugun shirin na APC shi ne amfani da EFCC wajen cin zali, cin zarafi da hantarar shugabannin PDP, wadanda ke hada kan 'yan Najeriya a aikin da ke gabansu, da nufin tilasta musu su sauke nauyin da ke kansu na jama’a su koma APC.

A cewar sanarwar, wannan yasa EFCC ta yi kokarin bata wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar da suka hada da; tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki; tsoffin gwamnonin jihohin PDP, ciki har da tsohon gwamnan jihar Abia, sanata Theodore Orji.

Hakazalika da tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson; takwaransa na jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso da sauran manyan jiga-jigan PDP.

Ta kuma koka kan cewa, takwarorinsu na APC da ke da irin wannan zarge-zarge sauran wadanda suka koma APC suna yawo cikin walwala.

Obasanjo bayan gana wa da PDP: Najeriya na iya tabarbarewa idan ba a kula ba

A wani labarin daban, Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Alhamis 19 ga watan Agusta ya bayyana kwarin gwiwa cewa har yanzu Najeriya za ta kai ga matsayi mafi girma kuma za ta sami matsayi mai kima a cikin hadin kan kasashen duniya.

Kara karanta wannan

Tonon sililin da Sanusi II ya yi wa Gwamnatin Buhari ya wanke mu inji Jam’iyyar PDP

Obasanjo ya fadi haka ne a Abeokuta yayin da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri da Prince Uche Secondus, Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Punch ta ruwaito.

Obasanjo ya bayyana taron a matsayin wanda ba a tsara shi ba yana mai bayyana cewa kofofinsa za su kasance a bude ga kowa da kowa ta hanyar matsayin da ya mallaka a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel