Bayan ya koma APC, ‘Ya ‘yan Jam’iyya sun fara rigima da Yakubu Dogara a jihar Bauchi

Bayan ya koma APC, ‘Ya ‘yan Jam’iyya sun fara rigima da Yakubu Dogara a jihar Bauchi

  • Wasu ‘Yan jam’iyyar APC a garin Tafawa-Balewa, sun kai karar Yakubu Dogara
  • ‘Ya ‘yan jam’iyyar sun ce Rt. Hon. Dogara ya karbe fam din neman takara a APC
  • Bangaren tsohon shugaban majalisar sun karyata tuhumar nan da ake yi masu

Bauchi - Wasu ‘yan jam’iyyar APC da aka bata wa rai a reshen karamar hukumar Tafawa-Balewa, da ke jihar Bauchi, suna kuka da Rt. Hon. Yakubu Dogara.

Jaridar Punch ta kawo labari cewa ‘ya ‘yan jam’iyyar suna zargin tsohon shugaban majalisar wakilan da yin karfa-karfa a zaben shugabanni da za ayi.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, ana zargin Rt. Hon. Yakubu Dogara ya karbe fam din shiga takarar zaben shugabannin APC na kananan hukumomi.

Mai magana da yawun bakin wadannan mutane, Alhaji Bala Burga, ya fitar da jawabi game da wannan batun a ranar Alhamis, 19 ga watan Agusta, 2021.

Kara karanta wannan

An yi karar Shugaban APC, Mala Buni, ana so Kotu ta tsige daukacin shugabannin rikon kwarya

Ayi hattara da abin da aka yi a Zamfara

“A matsayinmu na ‘yan jam’iyya masu bin doka, fusatattun ‘ya 'yanmu sun rubuta korafinsu, sun kai wa kwamitin sauraron kara domin ayi gaskiya da adalci.”
“Ya kamata duk wasu ‘yan APC su koyi darasi da abin da ya faru a jihar Zamfara, inda kotun koli ta tsige duka wadanda aka zaba a jam’iyya, ta ba PDP nasara.”

Yakubu Dogara a Aso Villa
Mai Mala Buni, Muhammadu Buhari da Yakubu Dogara Hoto: www.premiumtimesng
Asali: UGC

Hakan ya faru a 2019 ne saboda APC ta ki shirya zaben fitar da gwani kamar yadda doka ta yi tanadi.

Bala Burga ya fada wa ‘yan jarida cewa ya kamata a raba fam ne ga shugaban APC na karamar hukumar Tafawa-Balewa, amma sai aka ba Muhammad Tukur.

Menene martanin mutanen Dogara?

Muhammad Tukur na-kusa da Hon. Yakubu Dogara ne, wanda yanzu haka shi ne ‘dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabun Bogoro, Dass da Tafawa Balewa.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Rikicin cikin gidan da ya ke damalmala Jam’iyyar APC ya kara cabewa

Jaridar take cewa Tukur ya musanya wannan zargi, yace APC ta jihar Bauchi ta yarda cewa za a fito da shugabanni ne ta hanyar maslaha, kuma an tafi da kowa.

“Masu ruwa da tsaki a APC a Dass, Tafawa Balewa, da Bogoro sun biya kudin fam din su ne ta hannun jagoran jam’iyya, Dogara, aka ba ni kudi, na sayo masu.”

Dogara ya sake sauya-sheka, ya bar PDP

A shekarar da ta wuce ne aka ji tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara ya ya yi watsi da jam'iyyar PDP mai mulki a Bauchi, ya koma APC.

Da yake bayanin dalilin komawarsa APC da ya bari a baya, Rt. Hon. Yakubu Dogara ya zargi gwamnatin Bala Mohammed da kin cika alkawuran da ta dauka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel