Obasanjo bayan gana wa da PDP: Najeriya na iya tabarbarewa idan ba a kula ba

Obasanjo bayan gana wa da PDP: Najeriya na iya tabarbarewa idan ba a kula ba

  • Tsohon shugaban kasan Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana makomai Najeriya nan gaba
  • Ya bayyana haka ne bayan gana wa da shugaban jam'iyyar adawa ta PDP, Prince Uche Secondus
  • Ya kira Uche Secondus a matsayin mutum mai kaunar ci gaban Najeriya, kuma mai son kasa

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Alhamis 19 ga watan Agusta ya bayyana kwarin gwiwa cewa har yanzu Najeriya za ta kai ga matsayi mafi girma kuma za ta sami matsayi mai kima a cikin hadin kan kasashen duniya.

Obasanjo ya fadi haka ne a Abeokuta yayin da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri da Prince Uche Secondus, Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Punch ta ruwaito.

Obasanjo ya bayyana taron a matsayin wanda ba a tsara shi ba yana mai bayyana cewa kofofinsa za su kasance a bude ga kowa da kowa ta hanyar matsayin da ya mallaka a Najeriya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar

Obasanjo: Najeriya na iya tabarbarewa idan ba a kula ba
Tsohon shugaban kasa Obasanjo | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Obasanjo ya ce zuciyarsa ta cika da farin ciki saboda tattaunawar da aka yi tsakanin mutanen biyu ta ta'allaka ne kan ci gaban Najeriya ba wai kan siyasar jam'iyya ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Abu daya da Secondus ya fada min wanda tayi min dadi shine ko da yake yana nan a matsayin Shugaban PDP, amma ya zo ne don tattauna halin Najeriya."

Obasanjo wanda ya nuna damuwa game da halin da kasar ke ciki ya ce ci gaban kasar ya kamata ya kasance mai matukar muhimmanci ga duk mai kaunar al’umma.

Ya kara da cewa:

“Najeriya ba ta inda ya kamata ta kasance kuma tana iya tabarbarewa idan ba a yi abubuwan da suka dace ba.
"Duk da cewa yanayin na iya yin muni, amma ba abin a cire rai bane kuma da ba za a iya warkewa ba.

Kara karanta wannan

Olusegun Obasanjo yayi magana akan ta’addancin da ke ta'azzara a Najeriya

“Ni mai imani ne dangane da makomar Najeriya.
“Abin da kawai za mu yi shi ne mu hada hannu waje guda don gina ta tayi gaba.
"Na tabbata har yanzu Najeriya ta kasance mafi kyau kuma za ta kasance mai girma."

Akwai bukatar neman tallafi daga kasashen waje

Dattijon ya kuma jaddada bukatar neman tallafi daga kasashen duniya da kuma amfana da tarin gogewarsu.

Obasanjo ya bukaci Secondus da ya tabbatar da cewa bai sadaukar da kaunarsa ga Najeriya a kan siyasar bangaranci ba.

Ya kara da cewa:

“Inda ya zama dole a sanya hular jam'iyya, a sa; amma inda kuke bukatar sanya hula ta shugabancin Najeriya, don Allah ku sa."

Da yake mayar da martani, Secondus ya bayyana Obasanjo a matsayin dan kasa mai nagarta wanda ya dukufa kan batutuwan da suka shafi gina kasa, in ji jaridar Cable.

Shugaban na PDP na kasa ya tabbatar da cewa tattaunawar sa da Obasanjo ta ta'allaka ne kan Najeriya inda ya ce, "muna bukatar shawarar dattawa don ciyar da kasa gaba".

Kara karanta wannan

Obasanjo: Kara yawa da al'ummar Afrika ke yi na hana ni bacci cikin dare

Ya kara da cewa 'yan siyasa za su iya yin siyasa cikin sauki cikin yanayi na lumana.

A kalamansa:

"Na yi farin ciki da wannan ziyarar saboda dattijon mu ya sake farfado da fatan mu a Najeriya kuma za mu fita da sabon fata game da Najeriya."

Obasanjo: Shekaru 35 ciwon suga na azabtar dani ba kakkautawa, amma ban mutu ba

A wani labarin, Tsohon shugaban kasan Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ba bayyana siriin yadda ya ke lallaba rayuwarsa da ciwon suga a shekaru 35 da suka gabata, yayin da ya ce ciwon ya kashe abokan sa da dama amma shi gashi nan garau, Daily Nigerian ta ruwaito.

Cif Olusegun Obasanjo ya fede biri har wutsiya kan batun a ranar Laraba 18 ga watan Agusta a wani bikin da ya halarta na rufe taron ci gaban yara masu ciwon suga na jihar Ogun da aka gudanar a Abeokuta ta jihar ta Ogun.

Kara karanta wannan

Tsadar abinci: Dalilin da yasa 'yan Najeriya za su ci gaba da cin bakar wahala, in ji masana

Taron wanda Cibiyar Ciwon suga ta Talabi ta shirya, ya koyar da yara 21 da ke fama da ciwon suga mataki na 1 a jihar kan yadda ake fama da cutar.

A wani rahoto da Daily Trust ta rahoto, Obasanjo ya ja hankali da kuma shawartar yara da su kula da cutar suga matuka ta hanyar kiyaye salon rayuwa, yana mai cewa ciwon suga ba cuta ne da bai kai wa ga halaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.