Tonon sililin da Sanusi II ya yi wa Gwamnatin Buhari ya wanke mu inji Jam’iyyar PDP
- Jam’iyyar PDP ta ce gwamnatin APC ta durkusa tattalin arzikin kasa a shekaru shida
- Kola Ologbondiyan ya fitar da jawabi, inda yace Muhammadu Sanusi II ya yi gaskiya
- Tsohon Gwamnan bankin CBN yana zargin gwamnati mai-ci da maida kasar nan baya
Da gaskiyar Sanusi II - PDP
Abuja - Jam’iyyar hamayya ta PDP ta ce fallasar da tsohon gwamnan babban banki na kasa, Sanusi Lamido Sanusi, ya yi kwanaki, ya fito da gaskiyarta.
Sanusi Lamido Sanusi ya yi ikirarin gwamnatin APC da Muhammadu Buhari yake jagoranta ta rusa nasarorin da tattalin arzikin kasar nan ya samu a baya.
This Day ta ce jam’iyyar adawar ta fitar da jawabi, tana cewa kalaman da tsohon gwamnan na CBN ya yi, shi ne ra’ayin akasarin mutanen da ke kasar nan.
Sakataren yada labaran PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ya yi magana a ranar Laraba, 18 ga watan Agusta, 2021, yace lamarin tattalin arzikin ya kai intaha.
Ologbondiyan ya yi kira ga mutane su fito su rika magana ba tare da la’akari da kusancin kabila, siyasa ko wurin zama ba domin halin da ake ciki ya yi kamari.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Abin da jawabin PDP ya kunsa
“Mulkin APC da Buhari a shekaru shidan nan, ya yi nasarar ruguza duk wani bangare na cigaban kasa a dalilin gazawa, rashin gaskiya, sata, rashin hukunta masu laifi, wariya da wasu irin tsare-tsaren tattalin arziki da aka kawo da suka durkasa kasar.”
“A lokacin da PDP ta mika mulki, ‘Yan Najeriya za su tuna, tattalin arzikin Najeriya ya zarce kowane a Afrika, yana cikin mafi bunkasa a duk Duniya.”
“Jimillar karfin tattalin arzikinmu na GDP ya na Dala biliyan 574 a lokacin da aka ba Buhari mulki a 2015.”
“Abin takaici a shekaru shida da gwamnatin APC da Buhari ta yi, 33% ba su da aikin yi, an samu tashin farashi na 17.38%, kasuwancin Naira miliyan 60 ya ruguje, Naira ta fadi, Dala ta tashi daga N167 a 2015, zuwa N512 a gwamnatin APC maras kan gado.”
“Mafi bacin rai sh ne gwamnatin APC ta shafe nasarar da PDP ta ci wajen biyan bashin Najeriya, ta maida mu ‘yan maula, ta kai ana bin mu bashin N33.107tr.”
PDP ta ce rayuwa ta kara wahala a yau, mutum miliyan 82 ba su da abinci, litar fetur ya koma N165, buhun shinkafa ya kai N30, 000, haka sauran kayan abinci.
Me Sanusi II ya fada?
Da yake magana a kwanakin baya, tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II yace gwamnatin Najeriya ba ta samu wani cigaba a cikin shekaru 40 ba.
Sanusi II ya fadi haka ne a wani biki da aka shirya domin murnar cikarsa shekaru 60 a duniya. An yi taron ne a ranar Asabar 14 ga watan Agusta, 2021 a Abuja.
Asali: Legit.ng