Siyasar Kano: Rikicin cikin gidan da ya ke damalmala Jam’iyyar APC ya kara cabewa
- Rikicin cikin gida yana ta ƙara ƙamari sosai a jam'iyyar APC a jihar Kano
- Wasu ‘ya ‘yan jam’iyya sun ce an maida su ‘ya ‘yan bora a zaben da aka yi
- Sha’aban Sharada na cikin wadanda suke kukan ana yi masu rashin adalci
Kano – Rigimar da ta shiga tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano ta ki ci, ta ki cinye wa baya ga hayaniya da ake yi a kan zaben 2023.
Me ya jawo rigima a tafiyar APC?
BBC Hausa ta rahoto cewa jam’iyyar APC tana fuskantar rigingimu na cikin gida ne a dalilin zaben shugabannin da APC ke kan yi a fadin Najeriya.
Wannan rikici ya kara cabe wa bayan an gudanar da zabukan shugabannin mazabu, inda wasu bangare suka fito suna zargin an yi masu rashin adalci.
Jam’iyyar APC ta zabi ta fito da shugabanninta na mazabu ta hanyar maslaha, wanda hakan bai yi wa wasu bangare dadi ba, har ta kai sun kai korafinsu.
Ja-in-jar da zaben ya kawo ne ya sa shugabannin rikon kwarya na APC, suka aiko kwamitoci zuwa jihohin da aka samu sabani domin a nemi mafita.
Ba ayi mana adalci - Sha’aban Ibrahim Sharada
‘Dan majalisa mai wakiltar birnin Kano da kewaye, Honarabul Sha’aban Ibrahim Sharada yana zargin jam’iyyar APC mai mulki da kin karbar kukansu.
Da yake magana, tsohon hadimin na shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zargi masu rike da madafan iko da amfani da ‘yan daba wajen ganin bayansu.
Sha’aban Ibrahim Sharada ya kuma ce an hana su shiga babban ofishin jam’iyya da ke jihar Kano.
Kamar yadda BBC ta bayyana a ranar Alhamis, shugaban kwamitin da zai saurari koken ‘ya ‘yan APC a jihar Kano, Dr. Kabiru Ibrahim, ya musanya zargin.
Dr. Kabiru Ibrahim ya ce har zuwa yammacin 18 ga watan Agusta, 2021, babu wani wanda ya gabatar masu da korafi a kan zaben mazabun da aka shirya.
Kano za ta yi baki
A ranar Juma'a, 20 ga watan Agusta, 2021, shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnonin jihohi za su halarci auren Yusuf Buhari a Garin Bichi, Kano.
Masu mulki da shugabanni za su barko daga ko ina, su cika garin Bichi daga gobe domin 'dan shugaban kasa zai auri 'diyar Sarkin Bichi, Zahra Nasir Bayero.
Asali: Legit.ng