Fadar Shugaban Kasa Ta Maida Martani Kan Zargin da Sule Lamido Ya Jefa Wa Buhari

Fadar Shugaban Kasa Ta Maida Martani Kan Zargin da Sule Lamido Ya Jefa Wa Buhari

  • Fadar shugaban ƙasa ta maida martani ga tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, kan zargin da yayi
  • Mai magana da yawun shugaba Buhari, Mallam Garba Shehu, yace APC ba zata yi koyi a ɗabi'un PDP ba
  • Hadimin shugaban ya kuma yi kira ga tsohon gwamnan da ya fito ya faɗi yadda ya samu tikitin zama gwamna a 2007

FCT Abuja:- Kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, ya ƙalubalanci tsohon gwamna Sule Lamido, ya fito ya bayyana yadda Saminu Turaki ya sallama masa tikitin takarar gwamna a 2007.

Shehu ya faɗi hakane yayin maratani ga tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Lamido ya yi Allah wadai da karbar da Buhari yakewa gwamnoni da yan majalisu a fadar shugaban ƙasa idan suka sauya sheka zuwa APC.

Lamido ya kira abun da wata fuskar cin hanci da ta kunshi amfani da kayan gwamnati.

Tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido
Fadar Shugaban Kasa Ta Maida Martani Kan Zargin da Sule Lamido Ya Jefa Wa Buhari Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A martanin Garba Shehu, yace:

Kara karanta wannan

Gwamna Buni Ya Yi Watsi da Hukuncin Kotun Koli, Ya Na Nan Daram a Shugaban APC

"Inaga ya kamata gwamnan ya sake nazari a kan kundin tsarin mulki. Kafin zama shugaban kasa, kundin ya tanazar da abubuwa 4 da mutum zai cika."
"Na uku daga ciki ya nuna cewa duk wanda zai nemi ofishin sai ya kasance ɗan wata jam'iyya kuma jam'iyya ce zata ɗauki nauyinsa."
"Amma shugaban ƙasa, ba dai-dai yake da sauran ɗai-daikun mambobin jam'iyyarsa ba domin shi shugaba ne kuma jagora ne."

Shin doka ta hana shugaban ƙasa yin haka?

Shehu ya ƙara da cewa saboda wannan babu wata doka da ta hana shugaban ƙasa ya tarbi sabbin yan jam'iyyarsa kasancewarsa jagoran jam'iyya, Shehu yace:

"Wannan ba cin hanci bane, cin hancin siyasa shine a gabatarwa da gwamna takardun EFCC kuma a ba shi zaɓi, ko dai ya sauya sheka ko kuma ya fuskanci shari'a."
"Ko kuma kamar abinda ya faru a Jigawa, inda aka tilasta baiwa wanda zai gaji gwamna zaɓin da fadar shugaban ƙasa ta yi. Wannan shine abinda PDP ta yi a tsawon shekaru 16."

Kara karanta wannan

Ku Yi Murabus Daga Mukamanku Ko Na Sallameku, Gwamna Ya Gargadi Makusantansa

Mallam Shehu yace shugaba Buhari ya kai matakin da yake a yanzun ne bayan zama ɗan jam'iyya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanazar.

Shin amsar masu sauya sheka a fadar shugaba cin hanci ne?

Da yake martani kan maganar amsar masu sauya sheka cin hanci ne ta wata fuskar, Shehu ya shaidawa gwamnan cewa APC ba zata ɗauki dabi'un PDP ba.

Hadimin shugaban yace:

"Idan PDP ta mance abinda ya faru, a 2007 sun kafa kwamiti bisa jagorancin EFCC ta wancan lokacin, wanda zasu tantance duk waɗanda zasu tsaya takara a shekarar."
"Kwamitin bisa umarnin fadar shugaban ƙasa, yana watsar da duk wani ɗan takara da ba shi da kyakkyawar alaƙa da masu rike da mulki."
"Amma a ɓangare ɗaya, APC ta na janyo hankalin sauran shugabanni a wata jam'iyya ne ta hanyar lallashi da kuma cika alƙawarinta. Babu wanda aka tilastawa ya shigo APC."

A wani labarin kuma Ganduje Ya Gwangwaje Dukan Iyalan da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa da Tallafin Makudan Kudi

Kara karanta wannan

Zan Dau Tsattsauran Mataki Kan Jiga-Jigan Siyasa Dake Tada Hargitsi a Jihata, Gwamna

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya bada tallafin kudi dubu N200,000 ga kowanne ɗaya daga cikin iyalan mutum 18 da ambaliyar ruwa ta kashe a Doguwa.

Gwamnan ya kai ziyara ta musamman domin ta'aziyya ga iyalan mamatan ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel