Ku Yi Murabus Daga Mukamanku Ko Na Sallameku, Gwamna Ya Gargadi Makusantansa

Ku Yi Murabus Daga Mukamanku Ko Na Sallameku, Gwamna Ya Gargadi Makusantansa

  • Gwamna Douye Diri, ya gargaɗi yan majalisar zaratarwar jihar Bayelsa da su dakata da fara siyasar wuri
  • Gwamnan yacee duk wanda ya jefa kansa a cikin siyasar wuri ta 2023 ya janye ko gwamnati ta sallame shi
  • Ya kuma roke su da su maida hankali kan ayyukansu da gwamnatin jiha ta ba su umarni

Bayelsa:- Gwamnan Bayelsa, Douye Diri, ya gargaɗi makusantansa a kan fara bayyana kudirin su na siyasa gabanin zaɓen 2023, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana cewa ba zai tsaya wata-wata ba wajen sallamar duk wanda ya gano yana haka a cikinsu.

Gwamna Diri ya faɗi haka jim kaɗan kafin fara taron majalisar zartarwa a gidan gwamnati Ranar Laraba, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Diri ya nuna bacin ransa game da wasu ayyukan makusantansa wanda acewarsa sum fara buga gangar siyasa yayin da zaɓen 2023 ke gabatowa.

Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri
Ku Yi Murabus Daga Mukamanku Ko Na Sallameku, Gwamna Ya Gargadi Makusantansa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yancin siyasa a kundin mulki

Kara karanta wannan

Zan Dau Tsattsauran Mataki Kan Jiga-Jigan Siyasa Dake Tada Hargitsi a Jihata, Gwamna

Wani jawabi da kakakin gwamnan, Mr. Daniel Alabrah, ya fitar ya bayyana Diri na cewa duk da mutane nada yancin yin siyasa amma lokaci bai yi ba.

Yace: "Na yi matukar mamaki cewa kusoshin wannan gwamnatin har sun fara buga gangar diyasar 2023."

"Eh, kundin tsarin mulki ya basu yancin haka amma komai yana da lokaci. A halin yanzun muna kokarin cika alƙawurran da muka ɗauka wajen yakin neman zaɓen mu ne."

"Sabida haka ina umartar duk wanda yake da hannu a makamancin haka ya yi gaggawar janyewa. Idan har a shirye kuke ku cigaba da aiki da wannan gwamnatin to dole ku bi umarnin da ta baku."

INEC ta fitad da jadawalin zaɓe ne?

Gwamna Diri ya tunasar da jami'an gwamnatinsa cewa shekarar da ta gabata ta wuce salin alin saboda ɓarkewar annobar korona ba tare da gwamnati ta yi wani abu ba.

"Ina mamakin yadda kuka cusa kanku a cikin lamarin siyasa tun kafin hukumar zaɓe INEC ta fitad da jadawalin zaɓen 2023 dake tafe." inji shi.

Kara karanta wannan

Na gwammace in mutu da na bai wa Fulani filin kiwo, in ji wani Gwamna

Gwamnan ya roki yan majalisar zartarwar da suke da sha'awar fara siyasa a wannan lokacin da su yi murabus daga kujerunsu ko a sallamesu.

Ya yi kira ga duk wanda ya jefa kansa a cikin siyasar 2023 tun yanzun da ya gaggauta janye wa, ya bi umarnin da gwamnati ta bayar.

A wani labarin kuma Ruwan Sama Mai Tsanani Ya Lakume Rayuwar Mutum Biyu da Gidaje 1,500 a Jihar Katsina

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kastina (SEMA) ta bayyana cewa ruwan sama ya hallaka mutum 2 a Katsina.

Hukumar tace sama da gidaje 1,500 ne suka salwanta sanadiyyar ruwan saman a kananan hukumomi uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262