Ganduje Ya Gwangwaje Dukan Iyalan da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa da Tallafin Makudan Kudi

Ganduje Ya Gwangwaje Dukan Iyalan da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa da Tallafin Makudan Kudi

  • Gwamna Ganduje ya baiwa iyalan mutum 18 da ambaliyar ruwa ta cinye tallafin dubu N200,000 kowanne
  • Gwamnan ya bada wannan tallafin ne yayin da yakai ziyarar ta'aziyya ga iyalan ranar Lahadi
  • Gwamnan yayi addu'a Allah ya gafartawa mamatan tare da musu fatan shiga cikin rahamar Allah

Kano:- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya bada tallafin kudi dubu N200,000 ga kowanne ɗaya daga cikin iyalan mutum 18 da ambaliyar ruwa ta kashe a Doguwa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnan ya kai ziyara ta musamman domin ta'aziyya ga iyalan mamatan ranar Lahadi.

Ya kuma yi addu'ar samun rahama ga waɗanda suka rasu sanadiyyar ruwan sama mai tsanani, wanda ya haifar da ambaliya.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano
Gwamna Ganduje Ya Gwangwaje Dukan Magidantan da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa da Makudan Kudi
Asali: UGC

Ganduje yace:

"Lokacin da labarin ya iso garemu mun kaɗu sosai, muna addu'a Allah ya gafartawa waɗanda ruwan ya tafi da rayuwarsu."
"Muna musu Addu'a Allah SWT ya sanya su a cikin rahamarsa ta aljannatul Firdausi, Ameen"

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Maida Martani Kan Zargin da Sule Lamido Ya Jefa Wa Buhari

A ina Lamarin ambaliyar ta faru?

Waɗanda lamarin ya shafa sun fito ne daga garin Doguwa, ƙaramar hukumar Doguwa, mai nisan kilomita 200 daga cikin kwaryar birnin Kano, kamar yadda punch ta ruwaito.

Gwamna Ganduje yaje ta'aziyyar ne tare da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya, Alhassan Ado Doguwa.

Sauran sun haɗa da shugabannin jam'iyyar APC na jihar Kano, kwamishinoni da kuma wasu mambobin majalisar zartarwar jihar.

Iyalai sun yi wa Ganduje fatan Alkairi

Iyalan waɗanda abun ya shafa sun nuna matukar farin cikin su tare da godiya ga gwamna Ganduje bisa nuna kulawarsa.

Hakazalika sun yiwa gwamnan fatan Alkairi tare da addu'ar Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa.

A wani labarin kuma Matsalar Tsaro: Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Rediyo Najeriya

Yayin harin yan ta'addan sun yi kaca-kaca da motoci, gilasan jikin kofa, da na tagogin dake kafar watsa labaran.

Kara karanta wannan

Hushpuppi: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya gaya wa Buhari abin da ya kamata ya yi na mika Abba Kyari

Rahotanni sun bayyana ne cewa maharan sun kai wannan harin ne domin ɗaukar fansa biyo bayan wani farmaki da jami'an tsaro suka kai maɓoyar yan ta'addan a yankin Sasa ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel