Zan Dau Tsattsauran Mataki Kan Jiga-Jigan Siyasa Dake Tada Hargitsi a Jihata, Gwamna
- Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya sha alwashin daukar mataki kan yan siyasa
- Gwamnan yace ba zai zuba ido ya na kallo wasu yan siyasa su bata zaman lafiyar da jiharsa ke dashi ba
- Ya roki matasa da su kula sosai domin akwai yan siyasar da burin su bata musu rayuwa
Gombe:- Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya gargaɗi manyan yan siyasa da su daina tada yamutsi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ba zata lamurci a ringa hargitsin siyasa a faɗin jihar ba.
Yahaya ya fadi haka yayin da ya karbi bakuncin shugaba da yan majalisarsa da sauran masu faɗa a ji na ƙaramar hukumar Akko.
Wane yan siyasa gwamnan yake nufi?
Rahotanni sun nuna cewa akwai tsama tsakanin Sanata Danjuma Goje, da kuma Usman Kumo, wanda ke wakiltar mazaɓar Akko a majalisar dokokin jihar.
Kumo ya nemi takarar Sanata amma ya rasa ta ga Danjuma Goje a 2015 kuma an gano yana kokarin hambarar da Goje daga matsayinsa na jigo a siyasance.
Amma gwamnan yace ba zasu zuba ido su bar yan siyasa na haɗa kai da ɓata gari ba da sunan siyasa su tada zauna tsaye a jihar.
Gwamna na gaba da Sanata
Gwamna Yahaya ya sha alwashin ɗaukar mataki akan kowane mutum ko wata tawaga matukar aka tada rikici a jihar, kuma komai matsayinsa.
Yace: "Ba zan lamurci wannan ba, kuma ina fatan wannan ya zama na ƙarshe da zai faru karkashin kulawata a matsayina na gwamna."
"Saboda sanata yana ƙarkashin gwamna ta ɓangaren karfin iko da kuma a hukumance. Ba zan sake barin wannan lamarin da ya saba wa doka ya cigaba da faruwa ba."
Gwamnan ya roki matasan dake faɗin jihar da su kula da yan siyasar dake son gurbata musu rayuwa.
A wani labarin kuma Yan Bindigan da Suka Sace Basaraken Gargajiya Mai Daraja Ta Daya a Kaduna Sun Kira Iyalansa Ta Wayar Salula
Yan bindigan da suka sace basarake mai muhimmanci a masarautar Jaba, Kpop Ham, Gyet Maude, sun tuntubi makusantansa.
Ɓarayin sun kira iyalansa ta wayar salula, inda suka nemi a biya su kuɗin fansa har naira miliyan N100m, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Asali: Legit.ng