Rahoto: Manyan shari'u 5 da aka fi damuwa dasu saboda muhimmancinsu amma aka mance su

Rahoto: Manyan shari'u 5 da aka fi damuwa dasu saboda muhimmancinsu amma aka mance su

Tsokacin Edita: Wani lokaci a Najeriya, lamurra na zama kamar yayi, saboda idan abu ya kunno kai, to a lokacin kowa ke nuna damuwa akai. Wannan yakan kuma zama, idan abu ya dan kwana biyu, shikenan an manta kowa ya koma ga harkokinsa. Batun sharia, akwai wasu manyan shari'un da suka shahara a Najeriya saboda wasu dalilai, amma har yanzu tsit ake ji game dasu saboda wasu dalilai.

Jinkirin kammala wasu shari'un da suka 'shahara' a Najeriya ya haifar da damuwa tsakanin dangin wadanda abin ya shafa da masu lura da sanya ido akai, in ji rahoton Daily Trust.

Biyar daga cikin wadannan shari’un sune na Chukwudubem Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans; Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume da Abdulmuminu Danga, wani kwamishina a jihar Kogi, wanda ake zargi da cin zarafin wata budurwa.

Hakazalika da ta Andrew Ogbuja, wanda aka tuhuma da keta haddi da kisan matashiya Ochanya Ogbanje; yayin da kuma aka gurfanar da wani tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, kan zargin rashawa.

Kara karanta wannan

Dalilai da ke nuna alamun Nnamdi Kanu na iya fuskantar hukuncin kisa ko daurin rai da rai

Jama'a a shafukan sada zumunta na Najeriya sun bi diddigin labaran abubuwan da ake zargi na wadanda ake tuhumar bayan an gurfanar da su a kan laifukan.

Rahoto: Manyan shari'a 5 da suka shahara kuma aka yi tsit akansu duk da muhimmancinsu
Wasu daga cikin wadanda ake shari'a dasu | Hoto: dailyrust.com.ng
Asali: UGC

Abin da jama'a suka tsammanta shi ne cewa za a kammala shari'un cikin gaggawa domin a warware zarge-zargen da yawa na aikata laifuka da fahimtar jinkiri ko rashin adalci a kasar.

Masu sharhi sun gabatar da cewa duk da cewa wadannan shari'un suna yawo a kafofin watsa labarai da sararin tafukan hannun jama'a, dalilai da yawa na iya zama dalilai na jinkirinsu, wasu tun daga 2017.

Daga cikin matsalolin da suka jawo jinkirin akwai matsalolin da aka saba da su a bangaren shari'ar Najeriya, wasu kuma lauyoyi ne ke gabatar da su, ga zuwan annobar Korona, ga kuma zanga-zangar #EndSARS da yajin aikin kungiyar ma'aikatan shari'a a Najeriya (JUSUN).

Shari'un dake gaban kotu da aka jinkirta su

Daga cikin shari'un da ake cece-kuce akai sun hada da na wadannan:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Sanda Sun Cafke 'Yan IPOB a Wurin Shari'ar Nnamdi Kanu

1. Shari'ar Evans

Duk da hayaniyar da aka samu a shekarar 2017 ta kame wa da gurfanar da wani mai garkuwa da mutane, Evans, ba a kawo karshen shari'ar a 2021 ba.

An gurfanar da Evans, wanda aka fi sani da ‘Billionaire Kidnapper,’ an gurfanar da shi a bangarorin shari’a biyu na Babbar Kotun Jihar Legas, daya a Ikeja da kuma daya a Igbosere, kan wasu zarge-zargen satar mutane, kisan kai da yunkurin kisan kai.

Sauran wadanda aka gurfanar tare da Evans sune Uche Amadi, Ogechi Uchechukwu, Chilaka Ifeanyi, Okwuchukwu Nwachukwu da kuma Victor Aduba.

Duk suna fuskantar shari'a game ne da sace babban jami'in kamfanin Maydon Pharmaceutical Limited, Donatus Dunu, a shekarar 2017.

Duk da jikiri saboda Korona, jita-jita sun yi ta yaduwa cewa an yankewa Evans hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ya amsa laifuka da dama da ake zargin shi akai.

Amma bincike ya nuna cewa ba a yanke masa hukunci ba; ba a ma gabatar da karar tasa da mutane biyar da yake tare dasu ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sarakunan Yarbawa sun gana a jamhuriyar Benin kan batun Sunday Igboho

Majiyoyi sun ce kona kadarorin kotu, da suka hada da fayel-fayel na bayanai a yayin zanga-zangar #EndSARS ya shafi shari’ar ta Evans, wanda hakan ke nuna cewa tilas ne a ci gaba da shari’ar, tare da gabatar da sabbin takardu.

2. Shari'ar Wadume

Wadume na fuskantar shari'a a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume 13 na zargin ta'addanci da satar mutane a jihar Taraba.

Wadanda ake tuhuma tare da Wadume sun hada da Sufeto Aliyu Dadje, wanda ya kasance jami’in ofishi ne a hedikwatar ‘yan sanda da ke karamar hukumar Ibi a jihar Taraba.

Hakazalika da Auwalu Bala (Omo Razor); Uba Bala (Uba Belu); Bashir Waziri (Baba Gudu); Zubairu Abdullahi (Basho); Hafizu Bala (Maiwelder); Rayyanu Abdul da jami'an soja bakwai.

Jami’an sojin sun hada da Kyaftin Tijjani Balarabe; Staff Sgt David Isaiah; Sgt Ibrahim Mohammed; Kofur Bartholomew Obanye da Private Mohammed Nura.

Kana da Lance Kofur Okorozie Gideon; Kofur Marcus Michael; Lance Kofur Nvenaweimoeimi Akpagra; Staff Sgt Abdulahi Adamu da Ebele Emmanuel.

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Kafin yajin aikin na JUSUN da ya dakatar da shari’ar, ana sa ran Wadume zai gabata a gaban kotu a ranar 8 ga watan Mayu bayan masu gabatar da kara sun kammala komai na shari'ar a watan Maris tare da shaidu shida.

‘Yan sanda sun yi zargin cewa sojoji sun taimaka wajen sake shi bayan da wasu jami’an 'yan sanda daga Abuja suka kama shi, wadanda suka kai shi Ibi ta Jalingo a ranar 6 ga Agusta, 2019, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan sanda uku da fararen hula biyu.

Wadume ya tsere daga kamun ne a ranar 6 ga watan Agusta, 2019, amma an sake kama shi a Kano a ranar 19 ga Agusta, 2019.

Lamarin ya fuskanci kalubale bayan da aka raba jami’an sojan da ake zargi da kai harin na jami’an ‘yan sanda daga shari’ar sauran wadanda ake kara.

Bayan ware sunayen sojoji 10 da ake tuhumarsu da aikata laifuka a watan Yunin 2020, lauyan gwamnatin tarayya mai gabatar da kara, Magaji Labaran ya kawo sauye-sauye 13 da aka yi wa ragowar farar hulan.

Kara karanta wannan

Lauya ya ci alwashin maka Buhari a kotu idan ya hana 'yan Najeriya mallakar AK-47

Rikicin ya tilasta wa Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya jaddada cewa hukumomin soji za su gudanar da shari'ar jami'in bisa ga "tsarin shari'a na yanzu" tare da ba da tabbacin cewa za a yi adalci a cikin lamarin.

Malami ya bayyana cewa an ware sunayen sojojin ne domin kare hakkokin bil'adama na sauran wadanda ake kara a cikin lamarin, har sai lokacin da hukumar da ta dace ta kawo su - ta sojoji kenan.

Shaidun guda shida da suka bada shaida a shari’ar sun ba da labarin yadda aka yi nasarar kwato bindigogi shida daga Wadume da mutanensa.

Kamar yadda gwamnatin tarayya ta kammala shirin shari'ar, kotun ta sanya ranar 4 ga watan Nuwamba domin sauraran karar.

Lauyan da ke kare wanda ake kara a kan lamarin, Mohammed Tola ya ce:

“A shirye muke da batun; zai kasance don ba da tabbataccen tsaro.”

Kara karanta wannan

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

3. Shari'ar Ogbuja

Shari’ar fyade da kisan kai na wasu mutane biyu, wadanda suka kasance makusanta ga Ochanya Ogbanje mai shekaru 13 a wata Babbar Kotun Tarayya da ke Makurdi, Jihar Benue, ta gamu da koma baya, inda aka saurari karar karshe a watan Yunin 2020.

Jama'a sun harzuka a watan Oktoba na 2018 bayan Mista Andrew Ogbuja da dansa, Victor (a babba), da ake zargin sun yi wa Ochanya fyade, wanda ya kai ta ga mutuwa a ranar 17 ga Oktoba, 2018, saboda rikitarwa daga barnar da suka aikata mata.

Ogbuja ya kasance babban malami a Sashen Kula da Abinci da Gudanar da Otal, Makarantar Fasaha ta Jihar Benue, Ugbokolo, yayin da dansa, Victor, wanda a yanzu haka, ya kasance dalibin shekarar karshe a Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya, Makurdi.

Matarsa, Felicia, mai shekaru 43, ita ma hukumar da ke kula da hana fataucin mutane ta NAPTIP ta gurfanar da ita a kan tuhume-tuhume biyu da suka shafi cin zarafin mata da sakaci kan mutuwar Ochanya.

Kara karanta wannan

Kananan hukumomi biyu ne kawai ke cikin aminci a Kaduna - Sanata Sani

Wadanda ake tuhumar sun shigar da karar ba-kara a shari’ar a shekarar 2020, amma mai shari’a M. O. Olajunwo ya ki amincewa, inda ya ci gaba da cewa masu gabatar da kara sun gabatar da kwararan shaidu da za su bai wa wacce ake kara damar shigar da kara.

Maganar da ta ci gaba da kasance amma ga abubuwa da dama da suka shafi kotuna a Najeriya.

4. Shari'ar Danga

Sakamakon karshe na lamarin cin zarafin wata yarinya da aka ambata da suna Elizabeth da Kwamishinan Albarkatun Ruwa a jihar Kogi, Abdulmumini Danga, ya yi sanyi ba tare da bukatar bayanai ba duk da irin tsananin kulawa da la'antar da aka yi tayi akai.

An ruwaito cewa matar ta nemi taimakon kudi a wajen kwamishinan ga ‘yar uwarta ta shafin Facebook, wanda ake zargin ya kai ga sace ta da azabtar da ita.

Hakazalika an samu tabbataccen labarin cewa 'yan sanda sun gayyaci kwamishinan don amsa tambayoyi a yayin zafin shari'ar, wanda ba a sanar da jama'a cikakken bayani ba.

Kara karanta wannan

Hisbah: An kwamushe wasu mutane da ake zargin suna aikata luwadi a jihar Kano

Wata majiya ta shaida wa wakilin Daily Trust cewa an tura karar zuwa wata Babbar Kotun da ke Abuja, inda aka ba da belin kwamishinan.

Ba su gamsu ba, wasu kungiyoyi masu zaman kansu a jihar Kogi sun tuhumi cancantar belin a shari'ar da a ka’ida bai kamata a ba da beli ba.

5. Shari'ar Babachir Lawal

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya shiga rudani ne a wata kwangilar yankan ciyawa ta N544m da aka bai wa wani kamfani da ke da nasaba da shi, Rholavision Engineering Ltd da Josmon Technologies Ltd, shirin Shugaban kasa na Arewa maso Gabas (PINE)

An gurfanar da shi a kan tuhume-tuhume 10 a watan Fabrairun 2019 a gaban Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) kan wannan batu.

An sake gurfanar da shi a ranar 30 ga Nuwamba, 2020 a gaban Mai Shari’a Charles Agbaza sakamakon mutuwar tsohon alkalin da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Jude Okeke.

Kara karanta wannan

Gwamnan Gombe ya bayyana matakansa da ya dauka na kare dalibai daga sata a makarantu

Sauran wadanda aka gurfanar tare da shi kan sabon shari’ar sun hada da kaninsa, Hamidu Lawal, Suleiman Abubakar, Apeh Monday da kamfanonin biyu.

An yi amannar kammalar lamarin cikin gaggawa ya samu matsala ne daga wasu matsaloli da yawa da suka shafi bangaren shari'a a cikin 'yan kwanakin nan.

An dakatar da shari’ar Lawal a ranar 24 ga watan Yuni bayan kotu ta yi watsi da rahoton binciken da Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gabatar.

Lauyan da ke kare wanda ake tuhuma ya nuna adawa ga takaddar bisa hujjar cewa shaidun da aka kirkira na na’ura mai kwakwalwa sun karya ka’idar dokar Shaida, 2004.

Ana sa ran ci gaba da shari’ar a watan Oktoban bana.

Yawancin dalilai da ke haifar da jinkirin, in ji Lauyoyi

Da yake mai da martani kan abin da ya haifar da jinkiri a shari'o'in aikata laifuka a kasar, lauya Sunusi Musa, ya ce Dokar Gudanar da Laifuka (ACJA) a Najeriya ta tanadi sauraran kararrakin laifuka a kowace rana tare da kammala su cikin sauri.

Kara karanta wannan

Dr Isa Ali Pantami: Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijjah

Amma kowane lamari na iya samun dalilai daban-daban na jinkirinsu.

Shima da yake mayar da martani, Hameed Ajibola Jimoh ya ce cunkoson da ake samu a kotuna sakamakon rashin wadatattun alkalai na daga cikin abubuwan da ke kawo jinkiri a shari’un.

A cewarsa:

“Mun sha samun kararraki da yawa na kotuna da Korona, #EndSARS, har ma da wannan yajin aikin na JUSUN suka jinkirtasu. Don haka shekarar 2020 ta jawo jinkiri saboda kusan shekara daya a kotu bata yi aiki ba saboda dokar kiyaye tazara."

Ya kuma gano rashin tasirin cikakkiyar biyayya ga ACJA, jinkirin kiran shaidu da kuma hujjoji da kuma bata lokaci da masu gabatar da kara ke yi.

Shugaba Buhari zai gina manyan gidajen yari guda 3 a Kano da wasu jihohi

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya za ta gina sabbin cibiyoyi guda uku wadanda za su iya rage cunkoso na gidajen gyaran hali a kasar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a 23 ga watan Yulin 2021 a wajen bikin kaddamar da Hukumar Kula da Fursunoni ta Najeriya, da ke Hedikwatar rundunar ta Jihar Osun, a Osogbo.

Mista Aregbesola ya ce za a gina sabbin wuraren ne a Karchi ta Abuja, Kano, da Bori a jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel