Lauya ya ci alwashin maka Buhari a kotu idan ya hana 'yan Najeriya mallakar AK-47

Lauya ya ci alwashin maka Buhari a kotu idan ya hana 'yan Najeriya mallakar AK-47

  • Wani lauya mai rajin kare hakkin dan adam ya bayyana bukatar kowa ya mallaki bindiga
  • Ya ce idan shugaba Buhari yaki amincewa da haka, to lallai zai maka shi a kotu kan batun
  • Ya bayyana dalilansa na cewa ya kamata kowane dan Najeriya ya mallaki bindiga AK-47

Wani dan rajin kare hakkin dan adam, Malcolm Emokiniovo Omirhobo, ya yi barazanar maka Shugaba Muhammadu Buhari a kotu game da bayar da lasisin mallakar bindiga kirar AK-47 don kare kai.

Omirhobo a cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 8 ga Yulin 2021, ya bukaci shugaban da ya amince da mallakar bindigogi ga mutane don kare kansu, iyalai da dukiyoyinsu daga harin 'yan ta'adda masu rike da muggan makamai.

Da yake magana da Daily Trust, lauyan ya ce a shirye yake ya kalubalanci shugaban a kotu kan wannan batun a cikin kwanaki masu zuwa.

KARANTA WANNAN: Dalla-dalla: Bayanin yadda ake cike fom na neman ayyukan gwamnati 3 da ake dauka yanzu

Kara karanta wannan

Ka inganta tsaro, rangwantawa talakawa da rage farashin kaya, Sarkin Kano ga Buhari

Lauya ya ci alwashin maka Buhari a kotu idan ya hana 'yan Najeriya mallakar AK-47
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya ce:

“Ni dan Najeriya ne mai kiyaye doka, a likitance kuma mai hankali. Ni mutum ne mai dabi'a mai kaifin hali kuma ba a taba tuhuma ta cikin shekaru biyar da suka gabata ba game da wani laifi da ya shafi tashin hankali ko barazana."

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

Majalisar Dattijan Najeriya ta ce Ma'aikatar Sadarwa ta kafa wata cibiya da za ta rika aiki da butumbutumi da basirar na'ura don yaki da matsalolin tsaro a kasar, sashen Hausa na BBC ya ruwaito.

Najeriya dai na ci gaba da fama da matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane don kudin fansa da hare-haren 'yan bindiga musamman a arewacin kasar da ma ayyukan 'yan kungiyar Boko Haram/ISWAP a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kawo yanzu, sama da dalibai 1,000 ne aka sace daga makarantu a arewacin Najeriya tun daga watan Disamban 2020.

Kara karanta wannan

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

KARANTA WANNAN: Shekaru bayan da aka zargi Dino Melaye da digirin bogi, ya bayyana yin digiri na biyu

Yadda Gwamnati Ta Kame Sheikh Abduljabbar, Ta Turashi Magarkama Ya Yi Sallah

A wani labarin, Rahotanni da muke samu daga jihar Kano sun tabbatar mana cewa, gwamnati ta kame Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara bisa laifin batanci ga manzon Allah SAW.

Wata sanarwa da kwamishina na yada labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar ta nuna cewa hakan ya biyo bayan karbar rahoton farko da aka yi daga ofishin ‘yan sanda daga Ofishin Babban Lauya da kuma kwamishinan shari’a wanda ya shirya tuhuma kan malamin.

Daily Trust ta tattaro sanarwar na cewa:

"Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, babban malamin addinin musuluncin nan dake Kano ya shahara wajen tafsiri mai rikitarwa da maganganun da ake yi wa kallon na batanci ga sahabbai da kuma yin batanci ga Manzon Allah Muhammad (S.A.W) an gurfanar da shi a gaban kotu saboda laifin batanci."

Kara karanta wannan

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel