An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

  • Wasu 'yan fasa-kwaurin shinkafa sun hari jami'an kwastam, inda suka harbi wasu jami'ai
  • Rahoto ya bayyana cewa, a halin yanzu wasu jami'an na karbar kulawar asibiti a yankin da abin ya faru
  • Hakazalika, hukumar ta ytu Allah-wadai da irin wannan mummunan hari, ta kuma ci alwashin kame masu laifin

Akalla jami'an Kwastam uku da wani soja sun ji rauni lokacin da wasu masu fasa kwauri suka far musu a yankin Igboora da ke karamar hukumar Ibarapa ta jihar Oyo a ranar Juma'a.

Theophilus Duniya, Jami’in Hulda da Jama’a na Kwastam, sashin Ayyuka na Tarayya, shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar kuma ya ba manema labarai a Ibadan, Daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: Yadda Gwamnati Ta Kame Sheikh Abduljabbar, Ta Turashi Magarkama Ya Yi Sallah

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam
Jami'an kwastam | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Mr Duniya ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na daren Juma'a.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaban 'yan fashi ya kai hari kauyukan Zamfara, ya sace mutum 150 saboda an kama mahaifinsa

“Jami’an Kwastam din da suka ji rauni wadanda ke aiki ne a sashin A, Sashin Gudanar da Ayyuka na Tarayya, sun ga manyan motoci 8 dauke da shinkafar kasar waje da aka shigo da su ta barauniyar hanya da direbobinsu da fasinjojin da ke tare da su dauke da makamai suka far wa jami’an.
“Daya daga cikin maharan an harbe shi kuma an kwance makaminsa yayin da sauran suka koma da kayansu na fasa-kwauri.
"Ana ci gaba da bincike don kamawa da gurfanar da maharan, dukkan Jami'an Kwastam din da aka kaiwa harin da soja, ciki har da wanda aka harba a kai, suna karbar kulawa."

Rundunar kwastam ta yi Allah-wadai da harin

Ya ce mukaddashin kwanturolan sashin, DC Usman Yahaya, ya yi Allah wadai da harin kuma ya sake nanata kudurin hukumar na dakile fasa-kwauri, in ji Vanguard.

Rukunin, a cewar kwanturolan, ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba ko firgita da wadannan hare-hare da wasu masu aikata muggan laifuka dauke da makamai ke kai wa kan jami'an tsaro ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamandan Jami'an Tsaro a Igangan

KARANTA WANNAN: Shekaru bayan da aka zargi Dino Melaye da digirin bogi, ya bayyana yin digiri na biyu

Sojojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP, sun kwato makamai

A wani labarin, Dakarun sojin saman Najeriya sun lalata manyan motocin bindiga guda uku mallakar ‘yan kungiyar ta’addanci ta ISWAP yayin da suke tsallaka hanyar Damaturu zuwa Maiduguri domin aikata barna kan mazauna yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake yi wa manema labarai karin bayani a hedikwatar tsaro da ke Abuja ranar Alhamis kan ayyukan sojoji a cikin makonni biyu da suka gabata, Mukaddashin Daraktan, Harkokin Watsa Labarai na Tsaro, Brig Benard Onyeuko, ya ce sojojin sun kashe duk wadanda ke cikin motocin.

Onyeuko ya bayyana cewa, sojojin na sama, wadanda suka gudanar da ayyukan ta amfani da jirage masu saukar ungulu NAF Mi-35, sun yi aiki ne a lokacin da suka samu kiran gaggawa tare da tabbatar da cewa an kwato dukkanin makaman ‘yan ta’addan a yayin samamen.

Kara karanta wannan

Kyawawan hotunan ‘yar Najeriya da ta yi wuf da wani Bature, jama’a sun yi cece-kuce

Asali: Legit.ng

Online view pixel