Dalilai da ke nuna alamun Nnamdi Kanu na iya fuskantar hukuncin kisa ko daurin rai da rai
- Alamu sun nuna karara cewa, Nnamdi na iya fuskantar hukuncin kisa ko daurin rai da rai
- Wannan kenan duba da wasikar da gwamnatin Najeriya ta tura wa diflomasiyyar kasashe yamma
- A yau ne za a zauna don daddale halin da Nnamdi Kanu ke ciki, na hukunta shiu bisa laifukansa
Abuja - Akwai yiwuwar Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB, dake fuskantar manyan laifuka da hukuncinsu ya kai ga hukuncin kisa ko daurin rai da rai yayin da za a ci gaba da shari’arsa a yau Litinin, 26 ga watan Yuli.
Gwamnatin tarayya a cikin wata wasika da ta aika wa jami’an diflomasiyyar kasashen yamma ta zargi shugaban na IPOB da aiwatar da kashe-kashen jama’a a kasar.
Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, gwamnatin ta ce Kanu ya shirya kisan mutane akalla 60 da lalata dukiyoyi a wasu hare-hare 55 da aka kai hari a yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu cikin watanni hudu.
Wasikar wacce ke dauke da kwanan watan 26 ga Afrilu, 2021, ta yi zargin cewa mambobin kungiyar IPOB ne suka aikata ta'asar a kan umarnin da aka ce Nnamdi Kanu ne ya bayar a lokacin da yake boye a Landan.
Rigakafi kan Ta'addanci
Dokar sakamakon wannan zargi da ake wa Kanu shine idan aka same shi da laifi dumu-dumu, yana cikin kasadar a yanke masa hukuncin daurin rai da rai ko mafi muni; hukuncin kisa.
A cewar jaridar The Cable, Dokar Rigakafi kan Ta’addanci ta bayyana ko dai daurin rai da rai ko kuma hukuncin kisa saboda shiga ayyukan ta’addanci.
Sashe na 4 na Dokar Rigakafi kan Ta'addanci ya bayyana cewa:
''(1) Mutumin da da sane, ta kowace hanya, ya nemi ko bayar da goyon baya ga (a) aikin ta'addanci; ko (b) haramtacciyar kungiya ko kungiyar da ake zargi da ta'addanci a duniya. laifi a karkashin wannan Dokar zai iya daukar hukuncin daurin kurkuku na tsawon shekaru 20.
"(2) ba tare da nuna bambanci ba ga karamin sashe na (2) na wannan sashin ba, inda mutuwa ta afku daga duk wani aikin ta'addanci, to hukuncinsa shi ne hukuncin kisa.
"Saboda laifin cin amanar kasa, Sashe na 37 da sashe na 41 na dokar aikata manyan laifuka sun tanadi hukuncin daurin rai da rai ko hukuncin kisa."
'Yan Sanda Sun Cafke 'Yan IPOB a Wurin Shari'ar Nnamdi Kanu
A wani labarin, ‘Yan sanda a ranar Litinin sun fatattaki wasu mambobin kungiyar IPOB wadanda suka mamaye Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja don jin yadda za ta kaya a shari’ar Nnamdi Kanu, shugabansu.
Mambobin kungiyar da suka fusata sun mamaye kotun gabanin shari’ar tasa, inda wani rahoton The Cable ya ce tuni an kame wasu daga cikin mambobin na IPOB.
‘Yan kungiyar IPOB din suna ta rera taken nuna goyon baya ga Kanu tare da neman a sake shi.
Biyu daga cikinsu sun sanya tufafin yahudawa.
Wani mutum sanye da bakaken kaya harma yayi wa wasu manema labarai jawabi amma yayi magana ne da yaren Igbo, inji Daily Trust.
Sai dai, yayin da yawansu ya karu, ‘yan sanda suka afka wurin suka fatattake su. Ba a kawo Kanu kotu ba har zuwa lokacin da aka shigar da wannan rahoton.
Asali: Legit.ng