Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

  • Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata, 13 ga watan Yuli, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na kawo karshen rashin tsaro a Najeriya
  • Buhari, wanda ya karbi bakuncin mambobin Majalisar Tarayya a Abuja, ya nuna damuwa game da ayyukan ‘yan bindiga a kasar
  • Shugaban ya ce ikonsa na yin mulki don amfanin jama’ar Najeriya ya dogara da kyakkyawan hadin kai da hadin gwiwa tsakanin majalisa da bangaren zartarwa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya koka kan yadda rashin tsaro ke hana ci gaban kasar.

Jaridar The Nation ta ce Shugaban Kasar ya bayyana hakan ne a ranar Talata 13 ga watan Yuli yayin da yake karbar bakuncin sanatoci da mambobin majalisar wakilai a Abuja, babban birnin kasar.

Legit.ng ta ruwaito cewa Buhari ya ce matsalar tana tarnaki ga karfin gwamnatinsa na samar da ababen more rayuwa da kuma aiwatar da wasu manufofin ci gaba da gwamnatin ta sanya a gaba domin kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta gaza magance matsalar tsaro - Kukah ya fada wa Amurka

Ya ce a halin da ake ciki, ana bukatar daukar mataki mai tsauri da yanke matsaya mai tsauri wadanda dole ne a yi su da kwazo da kishin kasa, yana mai cewa irin wadannan matakan sun kasance hanya daya tilo da za su tabbatar da ci gaban Najeriya.

Buhari ya fadawa ‘yan majalisar cewa babu wani abin da za a bari domin kawo karshen rashin tsaro, inda ya sake jaddada shirye-shiryen gwamnatinsa na amfani da dukkanin wani ikonta wajen dawo da zaman lafiya da kuma gurfanar da masu aikata laifuka a gaban kuliya.

KU KARANTA: Shugaba Buhari na yiwa gwamnoninmu barazana, Jam'iyyar PDP

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari
Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari
Asali: Facebook

DUBA NAN: Gwamnatin Buhari ba ta iya magance rashin tsaro ba - Kukah ya fada wa Amurka

Gwamnatin tarayya za ta kawo karshen rashin tsaro nan ba da jimawa ba

A cewarsa, rashin tsaron ya kuma rage karsashin gwamnati na samar da ayyukan jin dadin jama'a da ake matukar bukata daga mutane da kuma jawo hankulan masu saka jari wadanda ke zaburar da kere-kere da samar da masana'antu da samar da ayyukan yi da kuma inganta tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

Ya ce:

“Rashin tsaro wanda ke haifar da ayyukan tsageru da na ‘ yan bindiga da satar mutane da aikata laifuka a birane iri-iri shi ne kalubale mafi wahala da muke fuskanta a yau.
‘’Wadansu daga cikin mutanen da suke haifar da wadannan abubuwan na rashin tsaro suna yi ne domin neman riba, wadansu kuma suna yi ne da sunan gurbatattun akidu. Ko ma menene dalilinsu da ma halayensu babbar barazana ce ga kasarmu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel