Jan Aiki: Shugaba Buhari zai gina manyan gidajen yari guda 3 a Kano da wasu jihohi

Jan Aiki: Shugaba Buhari zai gina manyan gidajen yari guda 3 a Kano da wasu jihohi

  • Gwamnatin shugaba Buhari ta ce za ta gina manyan gidajen yari a wasu jihohi da Abuja
  • Gwamnati ta bayyana haka ne a kokarin ta na rage cunkoso a gidan gyaran hali a Najeriya
  • Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka a jihar Osun ranar Juma'a data gabata

Jihar Osun - Gwamnatin Tarayya za ta gina sabbin cibiyoyi guda uku wadanda za su iya rage cunkoso na gidajen gyaran hali a kasar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a 23 ga watan Yulin 2021 a wajen bikin kaddamar da Hukumar Kula da Fursunoni ta Najeriya, da ke Hedikwatar rundunar ta Jihar Osun, a Osogbo.

Mista Aregbesola ya ce za a gina sabbin wuraren ne a Karchi ta Abuja, Kano, da Bori a jihar Ribas.

A cewar Ministan, kowanne daga cikin cibiyoyin zai kasance yana da kotuna don shari’ar fursunoni.

Kara karanta wannan

Minista Lai Mohammed ya magantu kan matsalolin kabilanci da addini a Najeriya

Jan Aiki: Shugaba Buhari zai gina manyan gidajen yari guda 3 a Kano, da wasu jihohi
Shugaba Buhari na Najeriya | Hoto: dailytrust.com.ng
Asali: UGC

Ya ce shirin Gwamnatin Tarayya shi ne fadada gina irin wadannan cibiyoyin zuwa shiyyoyin siyasa shida na kasar nan.

Ministan ya bayyana cewa aikin tuni a jihar Kano ya kusa kammala.

Mista Aregbesola ya ce lokacin da aka kammala ayyukan, za su taimaka wajen saukaka cunkoso tare da bunkasa karfin gudanar da kayayyakin gyaran hali na fursunoni.

Adadin da gidajen gyaran hali a Najeriya kan iya dauka na mutane a yanzu

Ministan ya bayyana cewa a halin yanzu cibiyoyin gyaran hali suna da girman da za su iya daukar fursunoni 57,278.

News Digest ta ce, ministan ya kara da cewa:

"Amma game da kirge na karshe, a farkon mako, akwai adadin fursunoni 68,747, wanda ke nuna yawan cunkoson yakai 18% cikin 100%."

Ya ce gwamnati na kokarin magance kalubalen cunkoson.

Rundunar sojin Najeriya ta karyata sakin 'yan Boko Haram, ta fayyace gaskiya

A wani labarin, a ranar Alhamis din da ta gabata ne Sojojin Najeriya suka karyata rahotannin sakin mayakan Boko Haram da aka kama a Borno, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Manyan shugabannin PDP sun sauya sheka zuwa APC, an saki sunayensu

Wata sanarwa dauke da sa hannun Onyema Nwachukwu, Darakta, Jami’in Hulda da Jama’a na Soji, ta ce rahotannin karya ne kuma wani mummunan yunkuri ne na dakile tarbiyyar sojoji da kuma tozarta sojojin na Najeriya.

Ya ce rundunar Soji ba ta da niyyar shiga batutuwa tare da wadanda suka kitsa labaran na karya amma za su yi kokarin daidaita bayanan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel