Kananan hukumomi biyu ne kawai ke cikin aminci a Kaduna - Sanata Sani
- Sanata Shehu Sani ya ce sace mutane ana da du ya zama bala’i a Jihar Kaduna
- Ya ce mazauna unguwannin da ke kewayen Kaduna sukan shigo cikin garin su kwana sai gari ya waye su koma
- Ya yi gargadin cewa idan babu wani matakin da aka dauka za a wayi gari a tarar babu ma Jihar Kadunan gaba daya
Tsohon dan majalisar dattijai, wanda ya wakilci mazabar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Tarayya, Sanata Shehu Sani, a jiya ya yi Allah-wadai da yadda 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a jihar ta Kaduna, wanda hakan ya haifar da mutane ke zama cikin fargaba da zullumi.
Yayin da yake amsa tambayoyi a shirin 'The Morning Show,' na tashar AriseNews, ya ce rashin tsaro ya zama ruwan dare a jihar kasancewar kananan hukumomi biyu ne kacal cikin 23 da ke jihar suke cikin aninci a halin yanzu.
Yana magana ne kan garkuwa da dalibai sama da 100 na makarantar Bethel Baptist High School, da ke Maraban Rido a Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna da kuma sace Hakimin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu, tare da iyalansa 10.
Koda yake, Hakimin da wadansu 'yan bindigar suka sace da safiyar Lahadi, an sako shi daga bisani.
Haka nan daya daga cikin daliban da aka sace na makarantar Baptist High School, Damishi Kaduna, an sako shi daga ‘yan bindigar.
Sani ya yi gargadin cewa idan ba a dauki kwararan matakai ba cikin gaggawa wajen dakile kashe-kashe da sace-sacen mutanen da ke faruwa a jihar, to za a wayi gari wata rana a tarar babu ma Jihar Kadunan gaba daya.
Yace:
“Suna tura shanunsu zuwa kan hanya kuma idan ka tsaya; kawai sai su fito daga daji su sace ka zuwa cikin daji.
“Da zarar bayan karfe 7 na dare ya yi, mutane da yawa daga gefen gari suna fita zuwa cikin gari sai gari ya waye suke koma wa. Wannan shi ne halin da muke ciki a yanzu,” inji tsohon Sanatan.
Shehu Sani ya ziyarci iyayen da aka sacewa yara
Sanata Shehu Sani yana daya daga cikin wadanda suka nuna tausayawa tare da yin kira da a yi wani katabus wajen ceto daliban da ma sauran mutanen da wadanda aka yi garkuwa da su a jihar.
Ko a makon jiya ma sai da ya taka sayyadarsa inda ya ziyarci makarantar inda iyayen daliban da suke cikin dimuwa suka taru domin gudanar da addu’o’in Allah Ya kubutar da yaran nasu.
A cewarsa, satar mutane ana garkuwa da su ta zama bala’ine da a kullum sai ya faru a jihar ta Kaduna ta yadda ma ba a bada rahoton faruwar wasu sace-sacen da dama.
Asali: Legit.ng