Rashin tashin bam ko 1 yayin sallah alamace ta dawowar ingancin tsaro, Fadar Buhari

Rashin tashin bam ko 1 yayin sallah alamace ta dawowar ingancin tsaro, Fadar Buhari

  • Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce alamun dawwamar ingancin tsaro ta nuna a Najeriya
  • Kamar yadda Femi Adesina ya wallafa, yace ba a samu kashe-kashe ko tashin bam ko 1 ba yayin sallah
  • Hadimin shugaban kasan yayi wa dakarun sojin kasar nan addu'ar Ubangiji ya basu kariya yayin da suke kare mu

Fadar shugaban kasa ta yi ikirarin cewa ba a rasa rai ko daya ba kuma babu bam ko daya da ya tashi yayin bikin babbar sallah balle a kai ga harin 'yan bindiga ko na 'yan ta'adda.

Femi Adesina, mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da hakan a wata wallafa da yayi a shafinsa na Facebook mai taken "Ubangiji ya albarkaci dakarunmu."

Kamar yadda takardar tace, Adesina ya nuna tabbacinsa na cewa kalubalen tsaron da ke addabar kasar nan baki daya ya kusa zama tarihi.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

KU KARANTA: Zamfara: Yari ya caccaki Buni, yace bai aminta da kwamitin rikon kwaryan APC ba

Rashin tashin bam ko 1 yayin sallah alamace ta dawowar ingancin tsaro, Fadar Buhari
Rashin tashin bam ko 1 yayin sallah alamace ta dawowar ingancin tsaro, Fadar Buhari. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan sa kai zasu jagoranci yaki da 'yan bindiga a Sokoto, Tambuwal

"Najeriya za ta ga karshen 'yan bindiga, ta'addanci, kashe-kashe, tashin-tashina, garkuwa da mutane. Zaman lafiyan da Najeriya za ta samu zai zama kamar korama.

"Kuma nan babu dadewa. Ko kun ji labarin tashin bam ko kisan mutane a yayin shagalin wannan sallar? A'a.

“Babu shakka muna samun cigaba. Nan babu dadewa zamu kai inda ya dace. Ubangiji zai kai mu kuma zai kare dakarunmu. Ameen."

Adesina yayi kira ga 'yan Najeriya da su yi addu'a ga sojojin kasar nan dake fuskantar 'yan bindiga, 'yan ta'adda da sauran miyagu da ke fadin kasar nan.

A wani labari na daban, mai rajin kafa kasar Yarabawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya gurfana a gaban wata kotun daukaka kara ta Kwatano saboda matsalar da ta hada da hukumar shige da ficen kasar.

Kara karanta wannan

Duk da ba ayi wa Ibo adalci a Najeriya, ba za mu goyi bayan Biyafara ba – Dattijon Neja Delta

Kotun ta bukaci a cigaba da tsare mata Igboho a yayin da za ta cigaba da sauraron karar a ranar Juma'a, Daily Trust ta ruwaito.

Amma kuma, matarsa, Ropo, wacce 'yar asalin kasar Jamus ce an saketa domin kotun tace bata kama ta da wani laifi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel