Duk da ba ayi wa Ibo adalci a Najeriya, ba za mu goyi bayan Biyafara ba – Dattijon Neja-Delta
Edwin Clark yace Nnamdi Kanu yana da abin korafi domin ana yi masu rashin adalci
Dattijon na Neja-Delta yace ba za su bi Ibo, su shiga kasar Biyafara idan aka barke ba
Clark yace ya kamata a rika ba Ibo mukamai, sannan a ba yankinsu karin wata jihar
Yankin kudu maso kudancin Najeriya ba zai zama cikin kasar Biyafara, har idan an barka kasar nan ba, wannan shi ne ra’ayin Cif Edwin Clark.
Edwin Clark ya bayyana cewa kungiyar IPOB ta na yin kuskure da ta ke cusa mutanen kudu maso kudu idan sun tashi kasa taswirar kasar Biyafara.
Dattijon yake cewa Nnamdi Kanu ya na fada ne a kan gaskiya, sai dai shugaban na kungiyar IPOB ya dauko wata hanya wanda da ba mai bulle wa ba.
KU KARANTA: Sunday Igboho ya shiga hannu, an damke shi ya na shirin zuwa Turai
A ra’ayin Edwin Clark, ba a yi wa Neja-Delta adalci wajen raba mukaman gwamnatin tarayya.
Har ila yau dattijon ya shaida wa BBC Pidgin cewa akwai bukatar a samu jihohi biyar a yankinsu, ganin sashen Arewa maso gabas su na da bakwai.
Da ake hira da shi, tsohon Ministan ya ce IPOB mai fafutukar samar da kasar Biyafara ta na da yara a kasa, amma ba ta dauki hanyar da ta dace ba.
“Na fada wa Kanu cewa a kan gaskiya yake, an yi watsi da mutanen yankin kudu maso gabas.”
KU KARANTA: Sheikh Abduljabbar ya shiga sahun Malaman da aka taba daure wa
“Su na da jihohi biyar ne rak, yayin da wasu bangarorin su ke da shida. Asali ma akwai wani bangare da ke da jihohi bakwai? Ko ta ina aka yi haka?
Kamar yadda The Nation ta rahoto, Clark ya ce ba a tuna wa da Ibo idan za ayi nadin mukamai, sannan kason da aka yi wa kasar ya sa ana cutar Ibo.
“Idan za a raba jami’a a kowace jiha. Za su samu biyar. Sauran bangarori za su samu shida. Yankin Arewa maso yamma zai tashi da jami’o’i bakwai.”
Asali: Legit.ng