FG bata mika bukatar dawo da Igboho Najeriya ba yayin da kotu a Kwatano ta tsare shi

FG bata mika bukatar dawo da Igboho Najeriya ba yayin da kotu a Kwatano ta tsare shi

  • Wata kotun jamhuriyar Kwatano ta gurfanar da mai assasa kafa kasar Yarabawa, Sunday Igboho
  • Sai dai lauyan Igboho, Yomi Aliyu, ya ce FG bata mika bukatar dawo da shi kasar Najeriya ba
  • Ya koka da yadda gwamnatin Najeriya ke rokon a adana mata Igboho har sai ta mika bukatar ta

Mai rajin kafa kasar Yarabawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya gurfana a gaban wata kotun daukaka kara ta Kwatano saboda matsalar da ta hada da hukumar shige da ficen kasar.

Kotun ta bukaci a cigaba da tsare mata Igboho a yayin da za ta cigaba da sauraron karar a ranar Juma'a, Daily Trust ta ruwaito.

Amma kuma, matarsa, Ropo, wacce 'yar asalin kasar Jamus ce an saketa domin kotun tace bata kama ta da wani laifi ba.

KU KARANTA: Jirgin NAF: Yadda jama'a suka taimaki matukin jirgin da 'yan bindiga suka harbo a Zamfara

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiya Ta Shawarci Sunday Igboho Da Nnamdi Kanu Su Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa

FG bata mika bukatar dawo da Igboho Najeriya ba yayin da kotu a Kwatano ta tsare shi
FG bata mika bukatar dawo da Igboho Najeriya ba yayin da kotu a Kwatano ta tsare shi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ndume na rokon kotu da ta tsame shi daga shari'ar Maina, ta bashi kadarorinsa

Igboho da matarsa sun shiga hannun hukuma ne yayin da suka dira filin sauka da tashin jiragen sama a Cardinal Bernardin dake Kwatano a ranar Litinin yayin da suke hanyarsu ta zuwa Jamus.

Amma kuma Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin Najeriya ta kasa shigar da bukatar son a dawo da Igboho gida Najeriya.

Yomi Alliyu, lauyan Igboho ya tabbatar da cewa FG ta kasa shigar da dalilinta a gaban kotun a ranar Alhamis a wata tattaunawar waya da aka yi da shi.

"Ba sakin matarsa kadai da aka yi ba, amma gwamnatin tarayya ta kasa shigar da bukatar son a dawo da shi gida. Suna kawai rokon jamhuriyar Benin da su tsareshi har zuwa lokacin da zasu kawo laifukansa. Wacce irin kasa ce wannan?," Aliyu ya tuhuma.

Kara karanta wannan

Yadda wasikar Jakadan Najeriya, Tukur Buratai ta taimaka wajen cafke Igboho a kasar Benin

Amma kuma ma'aikatar shari'a ta tarayya ta ce suna duba yadda zasu dawo da Sunday Igboho bayan kama shi da aka yi a jamhuriyar Benin.

Wani babban ma'aikaci a ma'aikatar wanda ya bukaci a adana sunansa yace tuni wata kotun Kwatano ta fara sauraron lamarin.

An kasa samun antoni janar na tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, a waya domin yin tsokaci amma kuma hadiminsa na yada labarai, Dr Umar Gwandu ya ce yana da bayanai kan lamarin.

A wani labari na daban, dakarun sojin Najeriya sun sheke wasu mutum uku da ake zargin 'yan Boko Haram ne tare da damke wasu 11 a cikin kokarin kawo karshen ta'addanci da suke yi a yankin arewa maso gabas.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasan, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin.

Ya ce an sun fatattaki 'yan ta'addan wurin Banki kan babban titin Miyanti inda suka hana 'yan ta'addan wucewa tare da miyagun makamansu.

Kara karanta wannan

Bayan Kame Sunday Igboho, Yarbawa sun magantu kan ra'ayin ballewa daga Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel