Zamfara: Yari ya caccaki Buni, yace bai aminta da kwamitin rikon kwaryan APC ba

Zamfara: Yari ya caccaki Buni, yace bai aminta da kwamitin rikon kwaryan APC ba

  • Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara ya ce bai amince da kwamitin rikon kwaryan APC na jihar ba
  • Kamar yadda yace, wadanda aka nada a halin yanzu ba ingantattun 'ya'yan jam'iyya bane kuma bai dace ba
  • Yari ya sha alwashin maka Mai Mala Buni a kotu domin yayi abinda baya cikin kundun tsarin mulkin jam'iyya

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, yayi watsi da kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC a jihar wanda aka baiwa alhakin juya akalar jam'iyyar a jihar.

Shugabannin jam'iyyar na kasa ne suka kafa kwamitin rikon kwaryan, Daily Trust ta wallafa.

Gwamna Mai Mala Buni, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar ya rushe zababbun shugabannin jam'iyyar na jihar kafin sauya shekar Gwamna Bello Matawalle.

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnatin Kano ta soke yin dukkan hawan sallah da shagulgula

Zamfara: Yari ya caccaki Buni, yace bai aminta da kwamitin rikon kwaryan APC ba
Zamfara: Yari ya caccaki Buni, yace bai aminta da kwamitin rikon kwaryan APC ba. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Jirgin NAF: Yadda jama'a suka taimaki matukin jirgin da 'yan bindiga suka harbo a Zamfara

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: An shawarci masarautar Kano da wasu masarautu su soke hawan sallah

Kafin wannan cigaban, Yari ne shugaban jam'iyyar a jihar Zamfara. Bayan rikicin da sauya shekar Matawalle ke tafe da shi, Buni ya kafa kwamitin rikon kwarya na mutum 3.

Amma Yari wanda ya caccaki Buni, ya ce bai aminta da kwamitin ba.

A wata tattaunawa da yayi da BBC, ya ce rushe shugabancin jam'iyyar a jihar Zamfara bai dace ba.

Tsohon gwamnan ya ce Buni bashi da ikon rushe shugabancin jam'iyyar dake karkashin ikonsa, inda yace hakan zai iya janyo wani rikici a jam'iyyar.

Ya kara da cewa, shugabannin rikon kwarya na jam'iyyar da aka nada yanzu ba asalin 'ya'yan jam'iyya bane.

Daya daga cikin hakkin kwamitin rikon kwaryan shine samar da yanayi da dukkan mambobin jam'iyya zasu sabunta rijistarsu.

Amma Yari yana barazanar daukar matakin shari'a inda yace an nada kwamitin rikon kwaryan ne yayin da aka yi karantsaye ga kundun tsarin mulkin jam'iyyar.

A wani labari na daban, Sanata mai wakiltar mazabar Borno ta kudu a majalisar dattawa, Ali Ndume a ranar Litinin ya bukaci babbar kotun tarayya dake zama a Abuja da su sahale masa zama wanda ya tsayawa Abdulrasheed Maina.

Kara karanta wannan

Idan ka biyewa Yariman Bakura zai kai ka ruwa, AbdulAziz Yari yayi kaca-kaca da magabacinsa

Idan zamu tuna, Maina, tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa ya gurfana a gaban kotu bayan hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon ta zargesa kan badakalar kudi har naira biliyan biyu. Read more:

Ndume, shugaban kwamitin sojoji na majalisar dattawa, yace baya son tsayawa Maina bayan da ya tsallake beli ya bar kasar baki daya, The Nation ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng