Da dumi-dumi: Sojoji 10 sun mutu yayinda jirgin sojojin Kenya yayi hatsari

Da dumi-dumi: Sojoji 10 sun mutu yayinda jirgin sojojin Kenya yayi hatsari

  • Jirgin sama mai saukar ungulu samfurin Mi 171e yana cikin aikin horo lokacin da ya sauko a yankin Ol Tepesi da misalin karfe 9 na safiyar Alhamis, 24 ga Yuni
  • Mai magana da yawun Kioko ya fitar da wata sanarwa wacce ta nuna cewa an lissafa dukkan fasinjojin sannan kuma an mayar da su wajen tsira
  • Kioko bai bayyana yawan fasinjojin da ke cikin jirgin ba ko kuma wadanda suka ji rauni amma ya tabbatar da an yi asarar rayuka

Wani jirgi mai saukar ungulu mallakar rundunar tsaron Kenya (KDF) ya yi hadari a Ngong, gundumar Kajiado.

Wani takaitaccen bayani daga KDF ya tabbatar da jirgin mai saukar ungulu samfurin Mi 171e yana kan aikin atisaye lokacin da ya fado a yankin Ol Tepesi da misalin karfe 9 na safiyar Alhamis, 24 ga Yuni.

KU KARANTA KUMA: Karin kudi a Najeriya yayinda FG, jihohi da kananan hukumomi suka raba N605.9bn a tsakaninsu a watan Mayu

Da dumi-dumi: Sojoji 10 ake tunanin sun mutu yayinda jirgin sojojin Kenya yayi hatsari
Sojoji 10 ake tunanin sun mutu yayinda jirgin sojojin Kenya yayi hatsari Hoto: Brite Adams
Asali: Facebook

A cewar KDF, jami'an sun fara aikin ceto nan take da suka samu labarin hatsarin na safiyar yau.

KDF ta fada a cikin wata sanarwa:

"Yau da misalin karfe 0900hrs, wani jirgi mai saukar ungulu na Mi 171e, a kan aikin atisaye ya fado a yankin OlTepesi da ke Ngong, yankin Kaiiado."

KU KARANTA KUMA: Gumi: Makiyaya suna satar yara ne kawai don kudi, sun fi yan IPOB

Hotuna da bidiyon da suka bazu sun nuna yadda jirgin ya tarwatse da wuta a yayin da yake fadowa.

Daga bisa a ranar, mai magana da yawun KDF din Zipporah Kioko ya fitar da wani bayani wanda ke nuna cewa an tatttara dukkan fasinjojin kuma an kai su wani wajen tsira.

Sai dai, Kioko bai bayyana yawan fasinjojin da ke cikin jirgin ba ko ma wadanda suka rasa rayukansu amma ya ce an dauke wadanda suka ji rauni zuwa Asibitin Dakarun Tsaro, Nairobi.

Kioko ya kara da cewa:

"Abin takaici, biyo bayan hatsarin, mun sami asarar rayuka. Hanyar sanar da iyalai don isar da bayanan da kuma jajen KDF na kan hanya.”

A halin da ake ciki kuma, wani rahoton na kamfanin dillacin labarai na Reuters ya bayyana cewa akalla sojojin Kenya 10 ne suka mutu a hatsarin.

Kafar yada labarai ta ce akalla 10 daga cikin sojojin sun mutu sannan wasu 13 kuma sun ji rauni, inda ta kara da cewa wadanda suka tsira an kai su asibitin sojoji da ke Nairobi don yi musu magani.

Shugaban hafsun sojojin kasan Najeriya ya mutu bayan watanni 4 a ofis

A gefe guda, mun kawo a baya cewa shugaban hafsun sojojin kasa na Najeriya, Laftana Janar Ibrahim Attahiru ya rasu.

Mabanbantan rahotanni sun tabbatar mana da mutuwar babban sojan kasar wanda ya shiga ofis a karshen Junairun 2021.

Jaridar PM News ta bayyana cewa Laftana Janar Ibrahim Attahiru ya mutu a sanadiyyar hadarin jirgin sama a ranar Juma’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel