Gumi: Makiyaya suna satar yara ne kawai don kudi, sun fi yan IPOB
- Makiyaya mutane ne na kwarai idan aka kwatanta da 'yan kungiyar IPOB in ji malamin addinin Islama, Ahmad Gumi
- A cewar fitaccen malamin, makiyaya suna sace yara ne kawai don kudi yayin da IPOB ke kashe jami'an tsaro
- Saboda haka Gumi ya bukaci 'yan Najeriya da su yi adalci ga masu aikata laifin kuma su daina kwatanta su da IPOB
Ahmad Gumi, malamin addinin Islama, ya ce rashin adalci ne idan aka kwatanta ayyukan makiyaya da na 'yan asalin yankin Biafra (IPOB).
Malamin, wanda aka san shi da samun damar zama da yan fashi da makami, ya ce laifukan makiyaya ko kusa basu kai na IPOB.
KU KARANTA KUMA: Najeriya za ta ci gaba da zama kasa daya da ba za ta rabe ba, Ganduje
Da yake magana a shirin gidan talabijin na Arise TV a ranar Laraba, Gumi ya yi kira da adalci a wajen kwatanta kungiyoyin biyu.
Ya ce daya "yana kashe mana gwanayenmu yayin da dayan yake satar yara don neman kudi ba kashe su ba".
“IPOB na kai hari ga‘ yan sanda, sojoji, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da sauran cibiyoyin gwamnati; suna kashe mutanenmu da ke aiki,” in ji shi.
”Sannan makiyaya suna satar yara ne ba don su kashe su ba sai don neman kudi; don haka ta yaya zaku kwatanta wani wanda yake kashe jarumanmu kai tsaye da wanda ke satar yara don neman kuɗi ba kashe su ba. Duba, muna buƙatar adalci a cikin abin da muke yi."
Sheikh Gumi ya faɗawa gwamnatin tarayya abin da za ta yi don hana satar ɗalibai a makarantu
A gefe guda, Sheikh Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin musulunci ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi sulhu da yan bindiga idan har tana son tabbatar da tsaro a makarantu, The Cable ta ruwaito.
Tun watan Disambar 2020, yan bindiga sun sace dalibai a kalla so shida a makarantu a yankunan arewa maso yamma da tsakiya inda suka sace a kalla dalibai da malamai 700.
Na baya-bayan ya afku a ranar Alhamis yayin da yan bindigan suka kai hari makarantar sakandare na gwamnatin tarayya da ke Birnin-Yauri, jihar Kebbi inda suka sace dalibai da malamai.
Asali: Legit.ng