Zulum Ya Bada Umurnin Rufe Manyan Makarantu Biyu a Borno

Zulum Ya Bada Umurnin Rufe Manyan Makarantu Biyu a Borno

- Gwamnatin jihar Borno ta bada umurnin rufe wasu kwalejin ilimi biyu a jihar na makonni biyu

- Gwamnatin ta ce ta dauki wannan matakin ne sakamakon rikicin da ya barke tsakanin ɗalibai kan dakunan kwana

- Gwamnatin ta ce matakin da ta dauka ya zama dole ne domin kare rayuka da dukiyoyin dalibai da malamai

Gwamnatin jihar Borno ta bada umurnin rufe wasu makarantun gaba da sakandare biyu a jihar bayan rikicin da ɗalibai suka yi na makonni biyu, The Punch ta ruwaito.

Makarantun da abin ya shafa sun hada da Kwalejin Ilimi ta Ibrahim Kashim, Maiduguri da Kwalejin Ilimi na Kimiyya da Fasaha ta El-Kanemi da ke Bama.

Zulum Ya Bada Umurnin Rufe Manyan Makarantu Biyu a Borno
Zulum Ya Bada Umurnin Rufe Manyan Makarantu Biyu a Borno. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Sojoji Sun Ragargaji 'Yan IPOB, Sun Kashe 7 Sun Kama Biyar a Rivers

Wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren ilimi na dindindin, Mr Mohammed Abatcha, a ranar Alhamis, a Maiduguri ya ce an dauki matakin ne domin kare ruruwar rikicin.

"Sakamakon rikici tsakanin ɗaliban Kwalejin Ilimi na Kashim Ibrahim, Maiduguri, da Kwalejin Ilimi na Umar Ibn El-Kanemi, Bama, a ranar 27 ga watan Mayun 2021 kan batun ɗakunan kwana,

"Ma'aikatar Kula da Makarantun gaba da sakandare tare da mahukunta a makarantun biyu sun yanke shawarar rufe makarantun na makonni biyu.

"Ɗaukan matakin ya zama dole domin daƙile ruruwar rikicin da kare rayuka da dukiyoyi a yayin da ake bincike kan abin da ya haifar da rikicin," a cewar Abatcha.

KU KARANTA: Buhari Ya Sabunta Naɗin Garba Abari a Matsayin Shugaban NOA

Rashin tsaro ya tilasta wa gwamnatin jihar Borno mayar da Kwalejin Ilimi ta Kimiya da Fasaha ta El-Kanemi, Bama, zuwa Maiduguri, suna amfani da gine-gine tare da Kwalejin Ilimi na Kashim Ibrahim.

A wani labarin daban, 'yan sanda a birnin tarayya Abuja sun kama Ahmad Isah, mai rajin kare hakkin bil adama kuma dan jarida, saboda shararawa wata mari da ake zargi da cin zarafin wata yarinya.

Isah, wanda aka fi sani da 'Ordinary President' ya dade yana gabatar da wani shirin rediyo da talabijin mai suna "Brektet Family".

Al'umma sun yi korafi a kansa ne bayan an gan shi cikin wani faifn bidiyo da BBC Africa Eye ta wallafa yana marin wata mata da ake zargin da cinnawa yar dan uwanta wuta a kai kan zarginta da maita.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel