Sojoji Sun Ragargaji 'Yan IPOB, Sun Kashe 7 Sun Kama Biyar a Rivers

Sojoji Sun Ragargaji 'Yan IPOB, Sun Kashe 7 Sun Kama Biyar a Rivers

- Rundunar sojoji ta ruwaito cewa an kashe mambobin kungiyar ESN/IPOB guda bakwai a jihar Rivers

- Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis 27 ga watan Mayun 2021 yayin wani samamen hadin gwiwa

- A cewar rahoton, jami'an tsaron sun kuma yi nasarar kama mutane biyar da ake zargin mambobin ESN ne

Wani rahoto da PM News ta wallafa ya nuna cewa sojojin Nigeria sun kashe a kalla jami'an Eastern Security Network, ESN, a wani gari a Rivers yayin samamen hadin gwiwa tare da DSS da NSCDC.

Legit.ng ta fahimci cewa sojoji sun kuma yi nasarar kama wasu mambobin na ESN guda biyar dauke da makamai. ESN kungiya ce ta mayakar kungiyar IPOB masu neman kafa kasar Biafara.

Sojoji da DSS Sun Kashe 'Yan IPOB Bakwai, Sun Kama Wasu Biyar a Rivers
Sojoji da DSS Sun Kashe 'Yan IPOB Bakwai, Sun Kama Wasu Biyar a Rivers. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Buhari Ya Sabunta Naɗin Garba Abari a Matsayin Shugaban NOA

A cewar rahoton, wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da jami'an sojoji suka fitar a ranar Alhamis 27 ga watan Mayu, tana cewa an kai samamen ne misalin karfe 6.15 na yamma.

Sanarwar ta ce:

"6 Div tare da hadin gwiwa da Keystone, DSS da NSCDC karkashin jagorancin Brig-Janar MD Danja sun kai samame mabuyar yan IPOB/ESN da ke dajin Agbochia da ke kan iyakar kananan hukumomin Eleme da Oyigbo a jihar Rivers."

KU KARANTA: An Kama Hadimin Gwamna Sule Da Wasu Mutum 16 Kan Satar Kayan Gwamnati

An kuma ruwaito rundunar sojojin na cewa ta kama tawagar yan IPOB/ESN yayin samamen.

Ta kara da cewa ta kashe mambobin IPOB/ESN bakwai yayin musayar wuta a samamen.

A wani labarin rahoton daban, gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya zargi tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu da zaman ɗan leƙen asiri da matsala ga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Da ya ke magana a gidan gwamnati a Port Harcourt a ranar Litinin, Wike ya ce Aliyu mutum ne da ya daɗe yana yaudarar jam'iyyarsu ta PDP ya kuma yi mata zagon ƙasa an 2015, The Nation ta ruwaito. Wike Ya Ce Aliyu 'Ɗan Leƙen Asiri' Ne Kuma Alaƙaƙai Ne Ga PDP.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin martani kan wata hira da aka yi da Aliyu a jaridun ƙasa idan ya zargi Wike da ƙoƙarin mayar da kansa uban jam'iyya kuma kai mulkin kama karya a PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164