Buhari Ya Sabunta Naɗin Garba Abari a Matsayin Shugaban NOA

Buhari Ya Sabunta Naɗin Garba Abari a Matsayin Shugaban NOA

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sabunta nadin Garba Abari, shugaban hukumar NOA

- Lai Mohammed, Ministan Labarai da Al'adu ne ya bada sanarwar sabunta nadin a ranar Alhamis

- Sabunta nadin da aka yi wa Abari za ta fara aiki ne daga ranar 25 ga watan Mayun shekarar 2021

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake nada Mr Garba Abari a matsayin shugaban hukumar wayar da kan 'yan kasa wato NOA, The Cable ta ruwaito.

Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed ne ya bayyana sake nadin cikin sanarwa da ya fitar a babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis.

Buhari Ya Sabunta Naɗin Garba Abari a Matsayin Shugaban NOA
Buhari Ya Sabunta Naɗin Garba Abari a Matsayin Shugaban NOA. Hoto: @thecableng

DUBA WANNAN: Wata Sabuwa: Farashin Burodi Zai Yi Tashin Gwauron Zabi, Masu Gidajen Burodi Sun Sanar

An fara nada Abari ne a kujerarsa a shekarar 2016 kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Hukumar ta NOA ce aka dora wa alhakin sanar da juma'a tsare-tsaren gwamnati da habbaka kishin kasa da hadin kai tsakanin jama'a.

A wata sanarwa da ya fitar a baya-bayan nan kan kallubalen tsaro a kasar, Abari ya yi kira ga shugabannin jama'a da matasa su rika wanzar da zaman lafiya a garuruwansu.

Ya ce ya kamata shugabannin mutane, siyasa, addini da tattalin arziki suyi gaggawar cimma matsaya kan bukatar ceto Nigeria daga yan bindiga, garkuwa da mutane, yan ta'adda, masu son raba kasa da kungiyar asiri domin ceto kasar daga rushewa. Idan muka bari Nigeria ta kone, dukkanmu za mu hallaka.

KU KARANTA: Masu Zanga-Zanga Sun Tare Hanyar Abuja-Kaduna Kan Sace Mutum 30 Da Yan Bindiga Suka Yi

"Rikici zai tarwatsa rayuwarmu da abubuwan da muke burin cimma ya kuma bar mu da aikin sake gina kasar mu.

"Ya kamata duk wani mai fada a ji a Nigeria, a wannan lokacin ya yi aiki domin hana rikici su kuma tabbatar sun zaburar da duk na kusa da su wurin ayyukan da za su samar da zaman lafiya a kasar," in ji shi.

Wannan sabon nadin da aka yi wa Abari zai fara aiki ne daga ranar 25 ga watan Mayun 2021 zuwa 2026.

A wani labari daban, Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai 19 a ƙauyen Yartsakuwa a ƙaramar hukumar Rabah na jihar Sokoto kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce ƴan sa-kan sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin da ƴan bindigan suka kaiwa garin.

Mazaunin garin, da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yan bindigan sun kai hari ne ƙauyen misalin ƙarfe ɗaya na ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel