Jiragen Yaƙi sun yi Luguden wuta kan Yan bindiga, Sun kashe sama da 24 a jihar Kaduna

Jiragen Yaƙi sun yi Luguden wuta kan Yan bindiga, Sun kashe sama da 24 a jihar Kaduna

- Gwamnatin Kaduna ta bayyana samun nasarar kakkaɓe wasu yan bindiga a wata maɓoyar su dake ƙaramar hukumar Birnin Gwari.

- Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya ce sama da yan bindiga 24 ne suka rasa rayukansu a harin da sojoji suka kai musu ta sama

- Rahoton bayan harin ya nuna cewa jirgin yaƙin da aka tura ya samu nasarar yin luguden wuta a maɓoyar yan bindigar ba tare da wata matsala ba

Kimanin yan bindiga 24 ne suka rigamu gidan gaskiya a wani luguden wuta da jami'an sojin sama suka yi a birnin gwari jiya Laraba.

KARANTA ANAN: Wani mutumi ya sheƙe tsohuwar Budurwarsa Saboda ta rabu da shi

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana a shafinsa na facebook.

A yayinda yake jawabi kan cigaban da aka samu, Samuel Aruwan ya ce an kashe yan bindiga sama da 24 a wani harin sama da aka kai musu a ƙaramar hukumar birnin gwari.

Rahotanni sun tabbatar da cewa rundunar sojin sama na 'Operation Thunder Strike' sun hallaka sama da yan bindiga 24 a wani hari da suka kai Unguwar Nacibi karamar hukumar Birnin Gwari.

Sojojin Sama sun yi Luguden wuta a kan Yan bindiga, Sun kashe sama da 20 a jihar Kaduna
Sojojin Sama sun yi Luguden wuta a kan Yan bindiga, Sun kashe sama da 20 a jihar Kaduna Hoto: @samuelaruwan
Asali: Twitter

Wannan na ƙunshe ne a rahoton sojojin da suka kai harin a jiya Laraba 7 ga watan Afrilu.

KARANTA ANAN: PDP tayi babban kamu yayinda Farfesa Jerry Gana da magoya bayansa suka sauya sheka zuwa jam’iyyar

A rahoton bayan harin, jirgin yaƙin ya kai hari ne a wata maɓoyar yan bindigar, kuma ya samu nasarar kashe dayawa daga cikin waɗanda ke wurin.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufa'i ya ji dadin wannan nasara da aka samu kuma ya jinjina ma rundunar sojin kan samun wannan gagarumar nasarar.

Gwamnatin ta tabbatar da zata cigaba da bibiyar maɓoyar tasu lokaci zuwa lokaci don sanin abubuwan dake faruwa.

A wani labarin kuma NSCDC ta kama makiyaya 50 da muggan Makamai a wasu Jihohin ƙasar nan

Kwamandan hukumar na ƙasa, Dr. Ahmed Audi ne ya bayyana haka a yayin miƙa ma wasu jami'ai masu zaman kansu shaidar gudanar da aiki.

Ya kuma ƙara da cewa hukumar sa zata cigaba da gudanar da aikinta yadda ya kamata domin ganin ta sauke nauyin da aka ɗora mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel