Wani mutumi ya sheƙe tsohuwar Budurwarsa Saboda ta rabu da shi

Wani mutumi ya sheƙe tsohuwar Budurwarsa Saboda ta rabu da shi

- Wani mutumi a Ibadan, babban birnin jihar Oyo ya cinna ma ɗakin tsohuwar budurwarsa wuta saboda ta ce bata buƙatar cigaba da soyayya da shi

- Rahotanni sun bayyana cewa mutumin mai suna Ahmed Saka ya daɗe yana barazanar kashe kansa da ita matar tun bayan rabuwarsu

- Hukumar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma ƙara da cewa har yanzun ana kan bincike

Wani mutumi mai suna Ahmed Saka ya kashe tsohuwar masoyiyarsa, Mutiat Oladele, tare da 'yayanta guda biyu ta hanyar cinna ma ɗakinta wuta.

KARANTA ANAN: Labari da duminsa: Ana harbe-harbe da bindiga a kusa da ofishin 'Yan Sanda a Aba

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba da daddare a Shogoye, yankin Idi-Arere dake Ibadan, Jihar Oyo kamar yadda PM News ta ruwaito.

An gano cewa Ahmed Saka da Mutiat Oladele sun kasance masu son junan su kafin ita Mutiat ta rabu da shi.

Saka ya daɗe ya na barazanar kashe kansa da kashe tsohuwar masoyiyar tasa saboda ta rabu dashi, wanda shine daga baya ya aikata hakan da daddare.

Bayan ya cinna wuta a ɗakinta, an gano wasu sauran 'yayan ta waɗanda suka ji muggan raunuka sanadiyyar wutar amma basu mutu ba.

Soyayya Ruwan Zuma-Wani mutumi ya sheƙe tsohuwar Budurwarsa Saboda ta rabu da shi
Soyayya Ruwan Zuma-Wani mutumi ya sheƙe tsohuwar Budurwarsa Saboda ta rabu da shi Hoto: medium.com
Asali: UGC

Yanzun haka waɗanda aka gano da sauran ransu suna asibitin Anglikan dake Molete suna amsar kulawa ta musamman.

KARANTA ANAN: Manyan Jami'an Sojin Ƙasar nan sun gana kan yawaitar Hare- Haren da ake kai ma hukumomin tsaro

Daga baya shima mutumin da ya saka wutar, Ahmed Saka, ya mutu.

Mai magana da yawun yan sanda, CSP Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis.

CSP Fadeyi ya ce: "Mutumin yaje ya cinna wuta a ɗakin matar saboda kawai tace bata bukatar cigaba da soyayya da shi."

"Mutumin da ya saka wutar shima ya mutu bayan faruwar haka, sannan akwai 'ya'yanta uku da sukaji munanan raunuka a dalilin wutar."

Fadeyi ya ƙara da cewa, jami'an yan sanda na cigaba da gudanar da bincike akan faruwar lamarin.

A wani labarin kuma Kara farashin mai da kudin haraji zai taimakawa gwamnati wajen magance matsalar tsaro, inji Ɗangote

Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, a ranar Laraba ya bayyana cewa gwamnati ba za ta iya aiki ba muddin ba'a biyan kudin haraji da kuma sayan man fetur a farashin da ya kamata.

Dangote ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: