PDP tayi babban kamu yayinda Farfesa Jerry Gana da magoya bayansa suka sauya sheka zuwa jam’iyyar

PDP tayi babban kamu yayinda Farfesa Jerry Gana da magoya bayansa suka sauya sheka zuwa jam’iyyar

- Farfesa Jerry Gana, tsohon ministan labarai da magoya bayansa sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

- Gana ya ce kasar nan ta tabarbare kuma tana bukatar ceto cikin gaggawa

- Ya kuma bayyana cewa babu wata gwamnati a jiharsa ta Neja dama Najeriya gaba daya

Tsohon Ministan Labarai, Farfesa Jerry Gana da magoya bayansa a jiya Laraba, 7 ga watan Afrilu, sun koma Jam’iyyar PDP.

Da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar a liyafar bikin dawowarsa PDP a hukumance a garin Bida da ke jihar Neja, Gana ya ce kasar nan ta tabarbare kuma tana bukatar ceto cikin gaggawa.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban karamar hukuma a Ribas

PDP tayi babban kamu yayinda Jerry Gana da magoya bayansa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar
PDP tayi babban kamu yayinda Jerry Gana da magoya bayansa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Gana, wanda mamba ne na kwamitin amintattu (BoT) na PDP a watan Maris, 2018, ya sauya sheka daga PDP ya kuma hade da jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).

Da yake magana a lokacin sauya shekarsa, tsohon ministan ya ce babu wata gwamnati a jiharsa ta Neja da Najeriya, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce, “Yau, ba rana ce ta lacca ba, ba rana ce ta kamfen ba, kawai muna so mu yi farin ciki cewa mun dawo da karfi; kuma za mu yi aiki tare sosai, za mu yi aiki tare yadda ya kamata, cewa za mu yi yakin neman zabe da karfi.”

KU KARANTA KUMA: Manyan shugabannin 'yan bindiga 4 sun mika kai a Katsina, sun bada shanu 45 da suka yi fashi

A wani labarin, Farfesa Ango Abdullahi, shugaban kungiyar dattawan Arewa (NEF), ya bayyana cewa arewa ba za ta yi amfani da kabila da addini ba wajen zaben shugabanni a 2023.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa yace ‘yan arewa sun koyi darasi mai tsadar gaske.

Legit.ng ta tattaro cewa Abdullahi ya bayyana cewa babu wani dan arewa da za a ba tabbacin samun goyon bayan yan arewa don kawai ya kasance dan yankinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng