Ku tsammaci cigaba a fannin tsaro nan babu dadewa, Mukaddashin sifeta janar Alkali

Ku tsammaci cigaba a fannin tsaro nan babu dadewa, Mukaddashin sifeta janar Alkali

- Sabon sifeta janar na 'yan sanda ya ce shugabancinsa zai baiwa 'yan sanda damar gyara matsalar tsaron Najeriya

- IGP Usman Alkali ya bayyana hakan ne a ranar Laraba bayan farfesa Osinbajo ya nada shi a gidan gwamnati dake Abuja

- A cewarsa, zai fifita kuma ya tabbatar da an samar da 'yan sandan yanki don kawar da matsalolin tsaron dake addabar al'umma

Sabon sifeta janar na 'yan sanda, Usman Alkali ya ce 'yan sanda a karkashin mulkinsa zasu tabbatar da bunkasa harkar tsaro a Najeriya.

Ya kara da bada tabbacin fifitawa da kuma tabbatar da 'yan sandan jihohi a karkashin mulkinsa.

IGP ya bayyana hakan ne a gidan gwamnati dake Abuja bayan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya nada shi.

KU KARANTA: Da duminsa: Ku mitsike min dukkan mambobin IPOB, Sifeta Janar Adamu

Ku tsammaci cigaba a fannin tsaron nan babu dadewa, Mukaddashin sifeta janar Alkali
Ku tsammaci cigaba a fannin tsaron nan babu dadewa, Mukaddashin sifeta janar Alkali. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

Shugaba Muhammadu Buhari ya daura Alkali a kujerar sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, inda ya maye gurbin Mohammed Adamu wanda ya kamata ya sauka daga madafin iko a watan Fabrairu, saidai an kara masa watanni 3.

Saidai Adamu bai karasa watanni ukun ba.

Alkali yace dama akwai tsarin 'yan sandan yankin tun baya, sai dai ba a aiwatar dashi ba, ya ce mulkinsa zai tabbatar da hakan.

'Yan Najeriya da dama sun dade suna kira akan tabbatar da 'yan sandan yankuna a kasar nan.

Sun yarda da cewa hakan zai taimaka wurin shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi bangarori da dama na kasar nan.

A matsayin daya daga cikin hanyoyin magance matsalar tsaro, kwanan nan gwamnatin tarayya ta amince da bayar da N13,300,000,000 don fara tabbatar da tsarin 'yan sandan yanki.

KU KARANTA: Saurayi ya gwangwaje budurwar da N24m ranar zagayowar haihuwarta, 'yan mata sun gigice

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin mataimakin sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, a matsayin sabon sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya.

Ya maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu, wanda wa’adin mulkinsa ya kare.

Ministan harkokin ‘yan sandan Najeriya, maigari Dingyadi ne ya sanar da hakan ga manema labaran gidan gwamnati.

A ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa’adin mulkin shugaban ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng