Da duminsa: Buhari ya nada Usman Alkali Baba a matsayin sabon IGP

Da duminsa: Buhari ya nada Usman Alkali Baba a matsayin sabon IGP

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin mataimakin sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, a matsayin sabon sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya.

Ya maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu, wanda wa’adin mulkinsa ya kare.

Ministan harkokin ‘yan sandan Najeriya, maigari Dingyadi ne ya sanar da hakan ga manema labaran gidan gwamnati.

A ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa’adin mulkin shugaban ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu.

Alkali zai karba ragamar mulkin ‘yan sandan Najeriya ne a take.

Karin bayani na nan tafe…

Asali: Legit.ng

Online view pixel