Da duminsa: Ku mitsike min dukkan mambobin IPOB, Sifeta Janar Adamu

Da duminsa: Ku mitsike min dukkan mambobin IPOB, Sifeta Janar Adamu

- Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya umarci 'yan sanda da su mitsike duk wani dan IPOB

- Ya sanar da jami'an tsaron da su yi amfani da makaman da suke da shi wurin ganin bayan duk wani mai tada kayar baya

- Mohammed Adamu ya bada wannan umarnin ne bayan ya ga hedkwatar 'yan sanda ta Imo da aka kone da gidan yari da aka balle

Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bada umarni ga jami'ai da kada su tausayawa masu rajin kafa kasar Biafra (IPOB), jaridar The Nation ta ruwaito.

Sifeta janar na 'yan sandan ya bada wannan umarnin ne yayin da ya ziyarci hedkwatar hukumar 'yan sandan Imo da aka kona da kuma gidan gyaran hali na Owerri a ranar Talata.

Adamu ya sanar da cewa dole ne 'yan sanda su yi amfani da makamansu wurin mitsike duk wani mai tada kayar baya.

KU KARANTA: 'Yan bindiga dauke da AK47 sun budewa jigon APC wuta a jihar Delta

Da duminsa: Ku mitsike min dukkan mambobin IPOB, Sifeta Janar Adamu
Da duminsa: Ku mitsike min dukkan mambobin IPOB, Sifeta Janar Adamu. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sojoji sun kubutar da dalibai 5 daga cikin 39 da 'yan bindiga suka sace a Kaduna

A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya ta bataliya ta 192 dake karamar hukumar Gwoza a jihar Borno sun samu nasarar kashe a kalla wasu 'yan ta'adda 12 da ake zargin 'yan Boko Haram ne, jaridar The Cable ta ruwaito.

Da tsakar daren Lahadi ne 'yan ta'addan suka kaiwa sansanin sojojin farmaki. Majiyoyi da dama sun sanar da The Cable cewa sojojin sun yi musayar wuta dasu.

"Rundunar Tango 9 sun yi gaggawar mayar da harin da 'yan ta'adda suka kai musu har suka kashe mutane 7 take yanke, hakan yasa suka ja da baya," Kamar yadda majiyar ta tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: