Saurayi ya gwangwaje budurwar da N24m ranar zagayowar haihuwarta, 'yan mata sun gigice
- Kafafen sada zumuntar zamani sun dauki zafi bayan ganin shagalin bikin murnar zagayowar haihuwar wata budurwa
- Budurwar mai amfani da suna Miss P tana tsaka da shagalin saurayinta ya gwangwajeta da kyautar N24,231,028
- Alamu sun nuna yadda budurwar ta rude ta kuma cika da farin ciki mara misaltuwa bayan ya bata kyautar
Ranakun zagayowar haihuwa su kan zo da albarkatu iri-iri musamman yadda mutane suke nuna wa mai shagali ko bikin so da kauna ta hanyar bayar da kyautuka na ban mamaki.
Wata 'yar Najeriya mai suna Miss P, wacce ranar haihuwarta ta zagayo taga ruwan naira, inda saurayinta ya gwangwajeta da kyauta mai yawa.
Kamar yadda ta wallafa, ta roki saurayinta kudi amma bata yi tunanin zai bata masu yawa haka ba. Ta wallafa wani bidiyo wanda aka ga tana shagalin a gida yayin da sauti mai dadin saurara ya bude ko ina.
KU KARANTA: Gwamnonin APC sun gwangwaje 'yan kasuwar da gobara ta shafa da N50m a Zamfara
Ba hakan kadai bane abin ban sha'awar, an ga inda wata takarda da take nade da kudaden kasar waje masu yawan gaske, wanda kimar kudin ya kai naira 24,231,028.
Take a nan jama'a suka fara tofa albarkacin bakunansu dangane da wannan kyauta ta ban mamaki.
KU KARANTA: Sojin Najeriya sun sheƙe ƴan Boko Haram 12 yayin da suka kai hari sansaninsu a Borno
A wani labari na daban, sojoji sun samu nasarar kubutar da dalibai 5 cikin 39 wadanda 'yan bindiga suka yi garkuwa dasu a FCFM dake Kaduna.
Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Samuel Aruwan ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Litinin, The Cable ta ruwaito.
'Yan bindigan sun yi garkuwa da daliban a makarantarsu dake Afaka, karamar hukumar Igabi dake jihar Kaduna a ranar 12 ga watan Maris.
A cewar Aruwan, yanzu haka sojoji sun dauki dalibai 5 zuwa asibiti don tabbatar da ingancin lafiyarsu.
Kamar yadda takardar tazo, "Sojojin Najeriya sun bayyana wa gwamnatin jihar Kaduna cewa sun kubutar da 5 daga cikin daliban FCFM, Afaka da aka yi garkuwa dasu da ranar nan, kuma yanzu haka suna asibiti ana kulawa da lafiyarsu."
Asali: Legit.ng