Zulum Ya Ce Ya Kamata Mulkin Nigeria Ya Koma Kudu a 2023

Zulum Ya Ce Ya Kamata Mulkin Nigeria Ya Koma Kudu a 2023

- Gwamnan Borno Farfesa Babagana Zulum ya ce yana goyon bayan mulki ya koma kudu a 2023

- Zulum ya yi kira ga jam'iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) ta karrama yarjejeniyar da aka yi a baya na mayar da mulki kudu

- Gwamnan Borno ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis wurin kaddamar da wani littafi kan tsaro

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya nemi a mayar da mulkin kasa zuwa kudacin Nigeria a gwamnati mai zuwa a shekarar 2023, Channels Television ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin jawabin da ya yi wurin taron tsaro da habbaka tattalin arziki wurin kaddamar da littafin da tsohon shugaban NIMASA, Dakuku Peterside ya wallafa mai taken "Strategic Turnaround".

2023: Ya Kamata Mulkin Kasa Ya Koma Kudancin Nigeria, Zulum
2023: Ya Kamata Mulkin Kasa Ya Koma Kudancin Nigeria, Zulum. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kano: 'Yan Hisbah Sun Kai Sumame Gidan Ɗaliban Jami'a, Sun Kama Mace da Namiji a Ɗaki Ɗaya

Ya yi kira ga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta karbi shawararsa ta amince da yarjejeniyar da aka yi a baya na cewa mulki zai koma kudu a 2023.

Gwamnan ya yi amfani da damar wurin danganta rashawa da gwamnatocin baya suka yi da Boko Haram.

Ya kara da cewa kuskuren da Nigeria ta yi ne ya janyo aka samu yan bindiga da ke adabar kasar.

Ya yi ikirarin cewa "Idan Nigeria ta yi koyi da wasu kasashen Afirka ta tallafawa kasashen da ke makwabtaka da ita, da an magance matsalar."

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 9 a Ƙananan Hukumomin Giwa da Birnin Gwari a Kaduna

A cewar gwamnan, karfin soja da sauya tsarin mulkin kasa ba za su magance matsalar ba, yana kira a samar da shugabanci na gari da sauya tunanin mutane.

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel