Na shirya: Budurwa ta tsayar da ranar da za a daura aurenta ba tare da miji ba, ta buga katin gayyata

Na shirya: Budurwa ta tsayar da ranar da za a daura aurenta ba tare da miji ba, ta buga katin gayyata

- Wata budurwa ta baiwa mutane da yawa mamaki yayin da ta saki katin gayyatar aurenta ba tare da miji ba

- Budurwar Jane Onyekwere ta ce ta gaji da tambayar da mutane ke yi mata na yaushe za ta yi aure

- Yayin da wasu suka shiga sashen ta na sharhi don tayata murna, abunda tayi ya sa wasu nishadi

Wata budurwa ta haddasa cece-kuce a shafin sada zumunta bayan ta saki katin gayyatar aurenta ba tare da sunan ango a kai ba.

Budurwar wacce aka bayyana da suna Jane Onyekwere, da take raba goron gayyatar bikin auren ta a Facebook, ta ce ta gaji da tambayar da mutane ke yi mata na yaushe za ta yi aure.

KU KARANTA KUMA: Manyan kasashe 17 mafi farin ciki a Afirka a 2021, Najeriya ce ta karshe

Daga katin gayyatar bikin da aka shirya yi a ranar Asabar, Afrilu, 12, bangaren da ya kamata ya kasance dauke da cikakkun sunayen ango an rubuta kalmar 'mijinta' a wurin.

Sakon Jane ya zo kamar haka: "Ina gayyatarku zuwa bikin aure na ..." Tunda mutane ba su yarda na huta da tambayar "Yaushe za ki yi aure ba ???" ..... Oya, ga ni nan .... Na shirya ."

Na shirya: Budurwa ta tsayar da ranar da za a daura aurenta ba tare da miji ba, ta buga katin gayyata
Na shirya: Budurwa ta tsayar da ranar da za a daura aurenta ba tare da miji ba, ta buga katin gayyata Hoto: Jane Onyekwere
Asali: Facebook

Mutane da yawa sun je ɓangaren sharhinta don taya ta murna cikin raha.

Queensley Kingsley ya rubuta:

"Lolz, ina taya ki murna, angon zai zo kafin ranar da aka sa...."

Anselem Anokwute ya ce:

"Allah ya albarkaci sabon gidanki. Ina taya ki murna."

KU KARANTA KUMA: Dole ku shafa mana lafiya a 2023, PDP ta aika sakon gargadi ga APC

Glory Rufus ya ce:

"Fatan alkhairi.

"Allah ya sa bani da data.”

A gefe guda, wani bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumunta wanda ke nuna Shugaba Samia Suluhu ta Tanzania tana cewa ba ta da wata matsala wajen mika wuya ga mijinta.

An ga bidiyon a shafin Twitter na wani mai suna @Goddieh_njihia wanda ya bayyana cewa mace ta farko da ta zama shugabar Tanzania abin kauna ce saboda kalamanta.

A cewarta, daga cikin rawar da suke takawa a gidan aure, ya kamata mata su mika wuya ga maza a matsayin nauyin kauna yayin da suma maza suke nuna musu kaunarsu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng