Wani tsoho dan shekara 70 ya ci ribar N3m a kiwon kifi

Wani tsoho dan shekara 70 ya ci ribar N3m a kiwon kifi

- Wani dattijo dan shekara 70 ya bayyana jin dadinsa da zuba jarin da yayi a harkar noman kifi

- Dattijon ya bayyana cewa ya fi karfin aikin gwamnati da za a bashi albashin N100,000

- Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta sanya hannu wajen karfafa sana'ar don samar da abinci mai tsafta da ayyuka ga matasa

Mista Ezra Amos, mai shekara 70 kuma tsohon ma'aikacin gwamnati daga yankin Dadin Kowa na Jihar Gombe ya ce ya samu sama da Naira miliyan 3 daga noman kifi a shekarar 2020.

Amos, wanda ya yi magana a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Dadin Kowa, karamar Hukumar Yamaltu-Deba, ranar Laraba, ya ce noman kifi yana biyan bukatunsa a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati da ya yi ritaya.

Ya ce jarinsa a harkar noma yana biyan shi fiye da lokacin da yake kan aiki, ya kara da cewa ya fara harkar kamun kifi ne tun daga shekarar 2012.

KU KARANTA: Matsi ya sa wasu direbobi bude tasha mai suna Tashar Buhari

Wani tsoho dan shekara 70 ya ci ribar N3m a kiwon kifi
Wani tsoho dan shekara 70 ya ci ribar N3m a kiwon kifi Hoto: Wikipedia
Asali: UGC

“A watanni hudun karshe na shekarar 2020, na samu Naira miliyan 1.4 daga kiwon kifi na. A cikin watanni hudun farko, na samu N750, 000, yayin da a cikin watanni hudun a tsakiya, na samu N850, 000."

Ya ce baya ga noman kifi, ya kuma tsunduma cikin kyankyasa da sayar da 'ya'yan kifi wanda a cewarsa ya samu kudi fiye da siyar da kifin.

"Da irin kudin da nake samu daga kiwon kifi, idan gwamnati ta ba ni aiki da ke biyan sama da N100,000 duk wata ba zan karba ba saboda akwai karin kudi a nan," in ji shi.

Ya ce a na da matukar bukatar kifi kuma “ko a jiya wani ya tambaya ko ina da karin kifin da zan sayar. Wasu lokuta masu saye har ma suna yin ajiyar kudinsu don sayen kifinmu kafin su isa girman da za a siyar dasu.

"Tare da kasuwar wacce ake samu da kuma tsananin bukatar kifi, duk wanda ya kuskura ya samu kudi."

Manomin kifayen, ya ce sana'ar yanzu ta fi tsada fiye da yadda take a baya sakamakon tsadar abincin da ya ce yana rage riba a cikin kasuwancin.

Amos ya ce da yawa daga cikin masu kiwon kifin a yankin Dadin Kowa / Kwadom suna bukatar goyon bayan gwamnati don raya kifaye a wani babban mataki don ba da gudummawa ga kokarin inganta samar da abinci da samar da ayyukan yi ga matasa.

Ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Gombe da ta bai wa manoman kifi horo kan yadda za su yi amfani da sinadaran abinci na cikin gida wajen yin kifin.

KU KARANTA: Ahmad Lawan ya bai wa gwamnati shawarin ta daina bijiro da uzuri

Amos ya shawarci matasa da masu yi wa kasa hidima a jihar da su yi amfani da damar da noma musamman kiwon kifi ya samar domin samun hanyar samun kudin shiga.

“Na sha shawartar matasa da su shiga harkar kiwon kifi ko aikin gona, kada su jira aikin fararen fata.

“Fara kananan kiwon kifi a cikin muhallinku a hankali zaku ga fa'ida. Ribar da ake samu a harkar noma ta fi wasu ayyukan da ake yi na fararen fata yawa,” inji shi.

A wani labarin, Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum ya sanya yara 1,163 na mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallinsu a wata makaranta a garin da aka kwato daga hannun masu tayar da kayar baya a jihar, The Sun ta ruwaito.

Gwamnan, wanda ya sanya ido a kan sanya yara 'yan gudun hijirar a garin Damasak, a ranar karshe ta ziyarar da ya kai yankin ranar Litinin, ya ce atisayen wani yunkuri ne na tabbatar da ci gaba mai dorewa.

Ya yi kira ga iyaye da su bar ‘ya’yansu su shiga makarantu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.