'Yan Bindiga Sun Kashe Ma'aikatan Kwallejin Fasaha Ta Kaura Namoda Biyu a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Kashe Ma'aikatan Kwallejin Fasaha Ta Kaura Namoda Biyu a Zamfara

- Wasu da ake zargi yan bindiga ne sun kai hari a karamar hukumar Kaura Namoda a Zamfara

- Maharan sun kashe mutane biyu sannan sun yi awon gaba da wata mata daga garin

- Yan sanda sun tabbatar da lamarin inda suka ce an baza jami'ai domin bin sahun yan bindigan

A kalla mutane biyu aka kashe sannan aka sace guda a wani sabon harin da aka kai a karamar hukumar Kaura Namoda da ke jihar Zamfara, TVC News ta ruwaito.

Wadanda aka kashe ma'aikata ne a Kwallejin Fasaha ta Kaura Namoda.

DUBA WANNAN: Gara Gwamnatin Abacha Da Na Buhari, Dr Obadiah Mailafia

'Yan Bindiga Sun Kashe Ma'aikatan Kwallejin Fasaha Ta Kaura Namoda a Zamfara
'Yan Bindiga Sun Kashe Ma'aikatan Kwallejin Fasaha Ta Kaura Namoda a Zamfara. Hoto: @TVCNews
Asali: Twitter

Wasu da ake zargin yan bindiga ne suka kashe su a safiyar ranar Laraba.

Yan bindigan sun afka garin misalin karfe 2 na daren Talata amma mutanen garin suka fatattake su.

KU KARANTA: Angon Da Ya Auri Matar Da Aka Saka Wa Rana Da Ƙaninsa, Soja, Da Ya Mutu Ya Magantu

Sun sake dawowa bayan awanni biyu sun kashe mutum biyu daga nesa sannan suka sace wata mata.

Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin amma ta ce jami'ai sun bazama neman yan bindigan.

Sun yi kira ga jama'a su kwantar da hankulansu su cigaba da gudanar da harkokinsu tare da basu tabbacin cewa rundunar yan sandan za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da zaman lafiya.

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164