Manyan kasashe 17 mafi farin ciki a Afirka a 2021, Najeriya ce ta karshe

Manyan kasashe 17 mafi farin ciki a Afirka a 2021, Najeriya ce ta karshe

- Kungiyar Hadin Gwiwar Cigaba ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoton farin ciki na duniya na 2021

- A bisa ga rahoton, kasar Finland itace a matsayin kasa mafi farin ciki a duniya

- A rukunin nahiyar Afrika kuwa, Najeriya ce ta 17 a kasashe mafi farin ciki

Rahoton farin ciki na duniya na 2021 ya tantance kasashe bisa la’akari da yadda suke farin ciki.

Rahoton wanda Kungiyar Hadin Gwiwar Cigaba ta Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa ya nuna kasar Finland a matsayin kasa mafi farin ciki a duniya.

Ya duba yadda cutar COVID-19 ta shafi tasirin mutane da jin daɗin su da kuma sakamakon da rufe kasashe ya haifar.

KU KARANTA KUMA: Ina durkusawa tare da mika kai ga mijina - Shugabar kasar Tanzania ta fadawa Mata a bidiyo

Manyan kasashe 17 mafi farin ciki a Afirka a 2021, Najeriya ce ta karshe
Manyan kasashe 17 mafi farin ciki a Afirka a 2021, Najeriya ce ta karshe Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Don kimanta kasashe, rahoton bugu na tara ya yi amfani da manuniya irin na karantar yanayin rayuwa, halin farin ciki da kuma na bakin ciki.

Ga cikakken yadda ya kasance a rukunin Afrika:

1. Mauritius

2. Libya

3. Congo

4. Kamaru

5. Senegal

6. Ghana

7. Nijar

8. Gambiya

9. Benin

10. Guinea

11. Afirka ta Kudu

12. Maroko

13. Algeria

14. Gabon

15. Burkina Faso

16. Mozambique

17. Najeriya

Lokacin da rahoton ya bayyana a shafin Twitter, daruruwan mutane sun kasance da abin faɗi. Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martaninsu a kasa:

@FighterThaps ya ce:

"Ina ganin 'yan Najeriya sun fi farin ciki saboda galibinsu suna zaune ne a kasar Afirka ta Kudu."

@mukuk_m ya ce:

"Mu yan kasar Zambia mun fi yan Najeriya da Afrika ta kudu farin ciki idan aka hada su."

@wahh_massa ya ce:

"Bana cikin farin ciki ba tun da aka haifeni. Ban san menene farin ciki ba. Hakan ya faru ne saboda an haife ni kuma ina zaune a Kamaru."

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Zamfara ya ƙara samun nasarar kuɓutar da wasu mutane huɗu da aka sace

@onthe1stof4th ya ce:

"Idan yanayin da Nijeriya ke ciki shine farin ciki, to ina tausayin sauran ƙasashe. Misali kowa na yi wa kowa ihu a nan kuma ku ce hakan farin ciki ne? Shikenan."

@freshkid_icon ya ce:

"Akwai wani magana cewa" rashin sani ni'ima ce "Yi bayanin dalilin da ya sa Kamaru ta kasance a nan. Idan har wannan jerin gaskiya ne to ina jajantawa sauran kasashen. Lallai kuna ganin rayuwa."

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng