Gwamnatin jihar Kwara ta bada umurni a bar dalibai mata su sanya Hijabi a Makarantun Mission

Gwamnatin jihar Kwara ta bada umurni a bar dalibai mata su sanya Hijabi a Makarantun Mission

- Bayan mako guda, gwamnatin Kwara ta sanar da matsayarta kan lamarin sanya Hijabi

- Wasu makarantun Mission a jihar na haramtawa dalibai mata shiga aji don sun sanya Hijabi

- Hakan ya tada kura tsakanin al'ummar Musulmi da Kirista a jihar

Gwamnatin jihar Kwara ta bada umurni ga dukkan makarantun gwamnati da makarantun da mabiya addinin Kirista suka assasa cewa kada wanda ya hana dalibai mata sanya Hijabi.

Hakazalika ya bada umurnin bude makarantu 10 da aka rufe makon da ya gabata.

Wannan na kunshe cikin jawabin da Sakataren gwamnatin jihar, Mamma Jibril ya saki ranar Alhamis.

A zaman da bangarorin Musulmai da Kirista sukayi da jami'an gwamnatin jihar, dukkansu sun ki janyewa daga matsayarsu.

Yayinda Musulmai suka tsaya kan bakansu cewa lallai sai an bar dalibai mata su sanya hijabi saboda dokar kasa ta amince da haka, Kiristoci sun ce sam basu yarda ba saboda ya kamata ayi la'akari da manufar kafa makarantun.

Amma gwamnatin jihar a hukuncin da ta yanke, ta ce ta yi kyakkyawan dubi ciki dukkan lamuran kuma ta yanke shawara.

Yace: "Saboda haka, gwamnati ta tabbatar da cewa daliba Musulma na da hakkin sanya hijabi a makaranta, kuma ta umurci ma'aikatar Ilimi da ta fitar da samfurin Hijabin da za'ayi amfani da shi a dukkan makarantun gwamnati da na Mission."

"Duk dalibar da take da niyyar sanya Hijabi a makarantu na da hakkin yin hakan."

KU DUBA: Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya ci gyaran matakin da Buhari, CBN, su ka dauka

Gwamnatin jihar Kwara ta bada umurni a bar dalibai mata su sanya Hijabi a Makarantun Mission
Gwamnatin jihar Kwara ta bada umurni a bar dalibai mata su sanya Hijabi a Makarantun Mission
Asali: UGC

KU DUBA: Kasar Rasha za ta rage kashi 50% na riga-kafin allurar 'Sputnik V' da ke maganin Kwaronabairus

A ranar Juma'ar da ta gabata ne Gwamnatin jihar Kwara ta bada umurnin kulle wasu makarantu mallakin coci a Ilori har sai an kammala tattaunawa kan lamarin hana dalibai sanya hijabi a makarantun.

Sakatariyar din-din-din na ma'aikatar ilimin jihar, Kemi Adeosun, ta saki jawabin cewa makarantun da hakan ya shafa sun hada da Cherubim and Seraphim (C&S) College, Sabo Okea d St. Anthony College, Offa Road.

Sauran sune ECWA School, Oja Iya, Surulere Baptist Secondary School da Bishop Smith Secondary School, Agba Dam.

Hakazalika akwai CAC Secondary School, Asa Dam, St. Barnabas Secondary School, Sabo Oke, St. John School, Maraba, St. Williams Secondary School, Taiwo Isale da St. James Secondary School, Maraba.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel