Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya ci gyaran matakin da Buhari, CBN, su ka dauka

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya ci gyaran matakin da Buhari, CBN, su ka dauka

- Farfesa Yemi Osinbajo ya ce bai dace a hana aiki da cryptocurrency ba

- Mataimakin shugaban kasan ya yi kira ga CBN da SEC su sake tunani

- Osinbajo ya bukaci hukuma ta rungumi fasahar, amma ta sa-idanunta

A yau Juma’a ne mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi kira a sa ido a yadda ake amfani da kudin ‘cryptocurrency’ a Najeriya.

Jaridar Vanguard ta rahoto Yemi Osinbajo ya na cewa abin da ya dace ayi shi ne a gyara harkar kudin yanar gizon, a maimakon a hana aiki da shi.

Farfesa Osinbajo ya bayyana haka ne a lokacin da ya tattauna a kan abubuwa da-dama, daga ciki har da sha’anin kimiyya da fasahar kudin yanar gizo.

KU KARANTA: Kasashe 7 da su ka haramta cinikin Bitcoin a Duniya

“Game da fasahar kudin yanar gizo da dukiyar cryptocurrencies, bari in fadi abubuwa biyu: na farko babu tantama cewa a nan da wasu ‘yan shekaru, fasahar blockchain za ta zama kalubale ga yadda aka saba aikin banki har da adanan kudi ta yadda ba a tunani.”

“Saboda haka dole mu shirya wa wannan sauyi da za a samu, kuma ya na nan zuwa ba da dade wa ba.”

"Yanzu haka ana yi wa kafofin cire kudi barazana, fasahar blockchain ya kawo damar da ta fi araha wajen aika kudi daga kasa zuwa kasa.” Inji Osinbajo.

Osinbajo yake cewa irinsu tsarin Ripple, sun zo wa bankunan da aka saba aiki da su da matsaloli.

KU KARANTA: Kasar Amurka ta ankarar da CBN game da Crypto

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya ci gyaran matakin da Buhari, CBN, su ka dauka
Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

“Na yaba da mataki mai tsauri da CBN, SEC da wasu hukumomi suka dauka domin hana yin ta’adi da cryptocurrencies, amma ya kamata su sake tunani.”

“Akwai bukatar a sa ido ne a nan.” Osinbajo ya yi kira a sa-ido a madadin a kawo dokar haramci. Ya ce: “Mu yi kaffa-kaffa wajen rungumar wannan fasaha.”

Kwanaki daya daga cikin ‘ya ‘yan mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo mai suna Fiyin Osinbajo, ya yi dogon rubutu a game da tsarin Cryptocurrencies.

A rubutunsa, Fiyin Osinbajo ya bayyana irin moriyar da ake ciki da tsarin Cryptocurrencies, ya ce bai kamata CBN ya hana mu’amala da wannan kudi a Najeriya ba.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel