Yanzu-yanzu: Alkali Binta Nyako ta kamu da cutar Coronavirus

Yanzu-yanzu: Alkali Binta Nyako ta kamu da cutar Coronavirus

- Alkali Binta Nyako na babban kotun tarayya, Abuja, ta kamu da cutar COVID-19.

- Kamfanin dillancin labarai, NAN, ta bayyana cewa za'a killaceta

Bayan shugaban Alkalan Najeriya da ya kamu makonnin baya, Mai Shari'a Hajiya Binta Nyako ta shiga jerin Alkalan Najeriya da suka kamu da cutar Korna.

A ranar 28 ga Junairu, Alkalin ta halarci taron karrama marigayi Alkali Ibrahim Watila da akayi a dakin taron Ukeje a karshen makon da ya gabata.

Alkali Watila ya mutu bayan gajeruwar rashin lafiyan da yayi.

DUBA NAN: Jerin abubuwa hudu da aka haramtawa makiyaya aikatawa a Ekiti

Yanzu-yanzu: Alkali Binta Nyako ta kamu da cutar Coronavirus
Yanzu-yanzu: Alkali Binta Nyako ta kamu da cutar Coronavirus Credit: Daily Trust
Source: Facebook

KU DUBA: Ba abinda zamu ragu da shi idan Fulani suka koma garinsu, kungiyar Afenifere

A bangare guda, gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, a ranar Laraba ya sanar da cewa ya samu waraka daga cutar Korona bayan kwanaki bakwai.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai a Makurdi, babbar birnin jihar, Channels TV ta ruwaito.

Ya mika godiyarsa da al'ummar jihar, abokansa, masoyansu a fadin tarayya bisa addu'o'insu lokacin da yake killace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel