Gwamnatin Kano za ta haramta talla da barace-barace a titunan jihar

Gwamnatin Kano za ta haramta talla da barace-barace a titunan jihar

- A wata sanarwa da Kwamishiniyar mata ta jihar Kano ta fitar ta bayyana cewa suna shirin kawar da mabarata daga titunan Kano

- Gwamnatin ta ware miliyan hudu don fara gudanar da shirin wanda za a kaddamar ranar Laraba

- Kwamishiniyar ta ce za su tabbatar sun kwashe duk wasu mabarata da masu tallace-tallace da ke takurawa mutane a titunan jihar ba

Gwamnatin Jihar Kano zata fara kwashe mabarata da masu tallace-tallace da kuma mutanen da ke yawo a tititunan jijar suna takurawa mutane ba tare da wani dalili ba, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishiniyar mata ta jihar, Dr Zahra'u Muhammad ce ta sanar da haka ranar Litinin a Kano.

Gwamnatin Kano za ta haramta talla da barace-barace a titunan jihar
Gwamnatin Kano za ta haramta talla da barace-barace a titunan jihar. Hoto: Vanguardngrnews
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa aka ga Buhari ba takunkumi a fuskarsa a Daura

Ta bayyana cewa tuni gwamnati ta tattauna da masu ruwa da tsaki ciki harda masu unguwanni da shugabannin addinai da kuma masauratun gargajiya guda biyar dake jihar don saukaka hanyar da za a bi wajen kawar da barace-barace a titunan jihar.

Saboda wannan aiki, gwamnati ta ware Naira miliyan hudu don gudanar da aikin a fadin jihar.

"Mun kammala shirye shirye don tsaftace tititunan Kano daga masu tallace-tallace da mabarata don tabbatar da tsafta da rage ayyukan ta'addanci a fadin tititunan.

"Za mu fara aikin daga ranar Laraba kuma zamu tabbatar da an tsaftace tititunan."

DUBA WANNAN: EFCC ta kama Shugaban Jami'ar Tarayya ta Gusau kan almundahar kwangilar N260m

Ma'aikatar kuma ta bayyana yadda ta karbi rukuni biyi na Almajirai daga Kaduna a baya bayan nan

Akwai maza da mata 47 da ke fama da rashin muhalli wanda za a taimaka musu a kuma kawar da su daga tititunan.

A wani labarin daban, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya goyi bayan Muhammadu Buhari a shekarar 2015 duk da cewa ya san 'bai san komai ba' Olagunsoye Oyinlola, tsohon gwamnan jihar Osun ya ce.

Mista Oyinlola ya yi bayanin cewa Mista Obasanjo ya yanke shawarar goyon bayan Mista Buhari ne saboda takaicin gwamnatin Goodluck Jonathan.

Duk da cewa (shi) Obasanjo ya san cewa dan takarar na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba zai iya tabuka wani abin azo-a-gani ba, amma duk da haka ya goyi bayansa bayan wasu jiga-jigan yan Najeriya sun matsa masa lamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel